Balle gidan yari: Jami'an tsaro sun sheke fursunoni 4, jami'i 1 ya jigata a kurkukun Osun

Balle gidan yari: Jami'an tsaro sun sheke fursunoni 4, jami'i 1 ya jigata a kurkukun Osun

  • Jami'an tsaro sun sheke 'yan gidan yarin Kosere da ke Osun har 4 har lahira yayin da suka yi yunkurin balle gidan su tsere
  • An gano cewa, yayin kokarin tserewan da safiyar Talata lokacin suna tsaftace gidan, sun jigata wani jami'in gidan da ke kula da su
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Osun ya tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai mai magana da yawun gidan yarin ya musanta faruwar hakan

Osun - 'Yan gidan fursuna hudu sun sheka lahira a gidan gyaran hali na Najeriya da ke yankin Kosere da ke Ile-Ife a wani yunkurin balle gidan da suka yi.

Wani babban jami'in tsaro, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Ile-Ife a ranar Talata, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutum 7 yan gida daya, da wasu mutum 17 a sabon harin jihar Kaduna

Jami'in ya ce wasu mazauna gidan fursunan sun yi yunkurin tserewa a yayin da suke aikin tsaftace gidan da safe, a hakan ne suka raunata wani jami'i.

Balle gidan yari: Jami'an tsaro sun sheke fursunoni 4, jami'i 1 ya jigata a kurkukun Osun
Balle gidan yari: Jami'an tsaro sun sheke fursunoni 4, jami'i 1 ya jigata a kurkukun Osun. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa, 'yan gidan yarin sun yi yunkurin balle gidan yayin da jami'an tsaro suka hana su, a take kuma aka kashe hudu daga ciki yayin da wasu da suka yi yunkurin tserewa suka koma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Premium Times ta ruwaito cewa, a yayin da aka tuntubi Solsa Adeotan, mai magana da yawun hukumar gidajen gyaran halin Osun, ya ce duk rade-radi ne babu gaskiya a lamarin.

Sai dai kuma, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce yana bukatar karin lokaci domin samo karin bayani.

Ana shirya balle gidan yarin Edo, mutum 3 sun tsere daga gidan fursunan Ilorin

Kara karanta wannan

Ana shirya balle gidan yarin Edo, mutum 3 sun tsere daga gidan fursunan Ilorin

A wani labari na daban, wani dan gidan gyaran hali da ke jiran hukuncin kisa da wasu ‘yan fashi guda biyu da ba a riga an yanke musu hukunci ba, sun tsere daga wani gidan yari da ke Ilorin, yankin arewa ta tsakiya a Najeriya, kamar yadda jami’an gidan yarin su ke kokarin warware zare da abawa akan balle gidajen gyaran halin da ya auku tun 2020.

Wadanda su ka tseren, Umaru Altine, wanda yake jiran hukuncin kisa saboda fashi da makamin da ya yi, sai Segun Nasiru da Isa Usman wadanda duk fashin suka yi su na jiran hukuncin kotu ne, kamar yadda jami’an suka sanar da Premium Times.

Sun tsere da safiyar Alhamis, 30 ga watan Disamban 2021 daga gidan gyaran hali da ke Mandalla a Ilorin, jihar Kwara bayan balle rodinan kurkukun kamar yadda wani jami’i ya ce.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara

Asali: Legit.ng

Online view pixel