Ana shirya balle gidan yarin Edo, mutum 3 sun tsere daga gidan fursunan Ilorin

Ana shirya balle gidan yarin Edo, mutum 3 sun tsere daga gidan fursunan Ilorin

  • Wasu 'yan gidan yari mai jiran hukuncin kisa da wasu biyu da ba a gama shari’arsu ba akan fashi da makami da suka yi, sun tsere
  • Lamarin ya auku ne a wani gidan yari da ke Ilorin, yankin arewa ta tsakiya wacce jami’an gidan yari suke kokarin warware batun bayan balle gidan yarin
  • Kakakin hukumar gidan yarin, Francis Enobore, ya tabbatar da tserewar nasu amma ya ce har yanzu ba a tabbatar da yadda lamarin ya auku ba

Ilorin, Kwara - Wani dan gidan gyaran hali da ke jiran hukuncin kisa da wasu ‘yan fashi guda biyu da ba a riga an yanke musu hukunci ba, sun tsere daga wani gidan yari da ke Ilorin, yankin arewa ta tsakiya a Najeriya, kamar yadda jami’an gidan yarin su ke kokarin warware zare da abawa akan balle gidajen gyaran halin da ya auku tun 2020.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

Wadanda su ka tseren, Umaru Altine, wanda yake jiran hukuncin kisa saboda fashi da makamin da ya yi, sai Segun Nasiru da Isa Usman wadanda duk fashin suka yi su na jiran hukuncin kotu ne, kamar yadda jami’an suka sanar da Premium Times.

Ana shirya balle gidan yarin Edo, mutum 3 sun tsere daga gidan fursunan Ilorin
Ana shirya balle gidan yarin Edo, mutum 3 sun tsere daga gidan fursunan Ilorin. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sun tsere da safiyar Alhamis, 30 ga watan Disamban 2021 daga gidan gyaran hali da ke Mandalla a Ilorin, jihar Kwara bayan balle rodinan kurkukun kamar yadda wani jami’i ya ce.

Premium Times ta gana da wasu na cikin gidan wadanda suka sanar da tserewar masu laifin amma ana ci gaba da bincike akan yadda asalin lamarin ya auku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin hukumar gidan yarin, Francis Enobore ya tabbatar da tserewar masu laifin, sai dai bai bayar da bayanai masu tsawo ba. “Na samu rahoto amma ban san wadanda lamarin ya shafa ba ko kuma yadda lamarin ya auku,” kamar yadda ya sanar da Premium Times.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara

Amma hukumar tana ci gaba da bincike kuma kwanan nan za a samu rahoto akai.

A watan Afirilun shekarar da ta gabata The Guardian ta ruwaito yadda gidan gyaran halin Mandala da ke da wurin zaman mutane 115 ya ke cike da mutane 500.

Baya ga wadanda suka tsere daga Ilorin, ma’aikatan gidan yarin sun shiga damuwa akan tsoron a balle gidan yarin jihar Edo, inda aka kai wa gidajen yari 4 farmaki tsakanin 2020 da 2021.

Wannan karon kuwa, ma’aikatan sirri na gidan gyaran halin sun ruwaito yadda masu laifi suke kokarin shigar da makamai cikin gidan don balle gidan watarana, Premium Times ta ga bayanai na cikin gidan akan hakan.

“Za su boye makaman a karkashin fulolluka sai a jefa musu ta katanga amma ba a sanar da lokaci ko kuma ranar da za ayi hakan ba,” kamar yadda rahotannin sirrin gidan yarin su ka bayyana.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa yara

Jami’an sirrin sun bukaci a samar da ma’aikatan tsaro da makamai na gani da fadi don su zagaye katangar kuma zasu dage wurin kulawa da kuma bayar da tsaro ga gidan yarin.

Kakakin ya ce bai tabbatar da batun balle gidan yarin ba a Benin amma ya ce gidan yarin ta na ankare da yuwuwar kai mata farmaki a kowanne lokaci.

Ya ce mafi yawan matsalar da gidajen gyaran hali ke fuskanta su ne matsalar mahara daga waje ba daga masu laifin cikin gidan ba.

Tsakanin 2020 da 2021, masu laifi daga gidajen gyaran hali fiye da 5,000 sun tsere daga gidajen yari mafi cunkoso a cikin jihohi 11 da ke Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel