Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC

  • Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Buhari za ta iya magance matsalolin tsaron kasar cikin watanni 17
  • Fayemi ya ce yin hakan zai sauya tunanin mutane da dama game da gwamnatin Buhari a dan lokacin da ya rage masa kan mulki
  • Sai dai shugaban kungiyar gwamnonin na Najeriya, ya ce babban abun da ke gabansa a yanzu shine kammala shugabancin jihar Ekiti lafiya ba wai takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce har yanzu gwamnatin Buhari na iya gyara matsalolin tsaron kasar cikin watanni 17.

Za a gudanar da babban zaben Najeriya a ranar 18 ga Fabrairu, 2023.

Da yake magana a wata hira da Arise News a ranar Asabar, Fayemi ya ce magance matsalar rashin tsaro zai sauya tunanin jama’a game da gwamnatin Buhari a cikin wa’adin da ya rage mata, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ba yaƙi na ke yi da Buhari ba, Sunday Igboho ya fitar da saƙon sabuwar shekara

Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC
Gwamnatin Buhari ta san abun yi don kawo karshen rashin tsaro cikin watanni 17 – Gwamnan APC Hoto: Thisday
Asali: Facebook

Fayemi ya ce:

"Idan za mu iya lalata wannan dodo na rashin tsaro, tunanin kasar zai canja sosai. Idan muka yanke shawarar bin diddigin wadannan mutane ba tare da la’akari da yancin dan adam da batutuwan da ka iya fitowa daga kasashen duniya ba, wadannan mutane ba fatalwa ba ne.
“Mun san inda yan fashin suke, don haka za mu iya shafe su sannan mu fara samun dama. Ba lallai a kawar da shi gaba daya a karkashin wannan gwamnati ba, amma kana iya yin wani bangare na hakan a karkashin wannan gwamnatin.
“A kawar da dukkan wadannan abubuwa da ke haifar da rudanin da suka jefa kasarmu cikin wannan yanayi. Har sai dai idan akwai masu cin gajiyar tattalin arzikin yakin a hukumomin tsaro, babu shakka sun san abin da za su yi kuma za mu iya gyara shi a cikin watanni 17."

Kara karanta wannan

'Yan Arewa sun magantu, sun bayyana yadda suka fi kaunar mulkin Jonathan fiye da Buhari

Da aka tambaye shi game da ra’ayinsa na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa, Fayemi ya ce: babbar damuwarsa a yanzu shine gamawa lafiya a matsayin gwamnan jihar Ekiti.

Ya ce kasar na cikin wani mawuyacin hali, kuma dole ne masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa su tashi tsaye wajen ganin an ceto kasar, ruwayar PM News.

“Akwai matakai da dama da za a dauka, na farko shine gamawa lafiya. Wannan zai dora ni kan hanyar neman shugabancin kasar.
“Amma ko shakka babu ba batun tsayawa ko rashin tsayawa takarar shugaban kasa ba ne Najeriya ke bukata a halin yanzu.
“Ina ganin muna bukatar wani matsayi na hadin gwiwa don ceto da kubutar da kasarmu daga tashe-tashen hankula, duk wani korafe-korafe a ciki da wajen kasar. Ya kamata mu hadu sannan mu taimakawa shugaba Buhari wajen ganin ya gama lafiya, wannan shi ne aikin a yanzu; ba wanda zai zama shugaban kasa ba. Idan lokaci yayi hakan zai faru.”

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wasu mata a Kaduna ranar jajiberin sabuwar shekara

Duk kashe-kashen da ake yi na matukar damuna, Buhari ya aike sakon jaje ga yan Najeriya

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatinsa ba zata gushe tana iyakan kokarinta wajen magance matsalar tsaron Najeriya ba.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a jawabin murnar sabuwar shekarar da ya saki da yammacin Juma'a.

Ya ce yan Najeriya su yi hakuri, gwamnatinsa na hada kai da kasashen dake makwabta wajen samar da mafita daga cikin lamarin rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel