Babu yadda za a yi in sake talauci a duniya, In ji shahararren mawaƙi, Timaya

Babu yadda za a yi in sake talauci a duniya, In ji shahararren mawaƙi, Timaya

  • Fitaccen mawakin Najeriya dan asalin Jihar Bayelsa, Inetimi Timaya Odon, da aka fi sani da Timaya ya ce ba zai sake yin talauci ba
  • Mawakin ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram a ranar Juma'a 31 ga watan Disambar shekarar 2021
  • Timaya ya shahara ne a shekarar 2005 bayan da ya fitar da wakarsa mai lakabin 'Dem Mama' daga bisani kuma ya cigaba da fitar da wasu wakokin

Shahararren mawakin Najeriya, Inetimi Timaya Odon, da aka fi sani da Timaya, ya ce babu yadda za a yi ya sake talauci a duniya.

The Egberi Papa 1 na Bayelsa ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na sada zumunta ta Instagram a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Wani mutum mai shekaru 42 ya mutu suna tsakar 'gwangwajewa' da budurwarsa a ɗakin otel

Ba zan sake yin talauci ba a duniya, In ji shahararren mawaƙi, Timaya
Ba zai yi wu in sake yin talauci ba a duniya, Timaya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da ya wallafa wani hoto, ya masa lakabi da 'wasu abubuwan ba za su sake faruwa bane. Kamar a ce in talauce. Ba zai yi wu ba! Sam sam."

A shekarar 2015 Timaya ya yi fice

Timaya ya shahara ne a shekarar 2005 bayan da ya fitar da wakarsa mai lakabin 'Dem Mama'

Ya yi wakan ne bisa farmakin da sojoji suka kai garinsu inda ya ce sun halaka mutane da dama.

A wurin taron baje kolin wakoki da aka yi makonni da suka gabata, Timaya ya bada labarin gwagwarmayar da ya sha lokacin da ya ke yaro.

Ya bayyana cewa ya sha matukar wahalar rayuwa yana yaro lokacin yana tallar ayabar Plantain, ya kara da cewa jajircewa da rashin karaya ne sirrin samun nasara da arziki.

Kara karanta wannan

Kaduna: Isa Ashiru, tsohon dan takarar PDP, ya bayyana niyarsa na sake fitowa takarar gwamna

Arewa TikTok: Bayan lakaɗawa 'Suddenly' duka har gida, ƴan sandan Kano sun shiga tsakani

A wani labarin, Rikicin TikTok ya janyo wasu abokan hamayya biyu na arewacin Najeriya, Aisha Zaki da Suddenly sun fara ba hammata iska, The Cable ta ruwaito.

Su biyun sun fara tara mabiya ta kafar wanda hakan ya janyo gagarumin tashin hankali har mabiyan daya su ka titsiye daya tare da zane ta har gida.

BBC Pidgin ta bayyana yadda mabiyan Aisha Zaki su ka bi Suddenly har gida su ka dinga jibgar ta sannan su ka wallafa bidiyon dukan nata a kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel