Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, Kungiyar kwadago a sakon sabon shekara

Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, Kungiyar kwadago a sakon sabon shekara

  • Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta yi kira ga ma'aikata su shirya tsaf don fito-na-fito da Gwamnati kan karin farashin mai da lantarki
  • NLC ta yi Alla-wadai da Gwamnonin wasu jihohi bakwai da har yanzu basu fara biya ma'aikata maf karancin albashin N30,000 ba
  • NLC ta sanar da ranar zanga-zangar gargadi a dukkan jihohin Najeriya 36 da kuma na musamman a birnin tarayya Abuja

Abuja - Kungiyar Kwadagon Najeriya NLC, ta lashi takobin cewa yan Najeriya ba zasu yarda da wani sabon karin farashin man fetur ma da sunan cire tallafin mai.

NLC ta yi kira ga ma'aikata da yan Najeriya su shirya zanga-zanga kan wannan abu da gwamnati ke shirin yi.

Shugaban NLC, Ayuba Wabbab, ya bayyana hakan a jawabin sabon shekara da ya saki ranar Asabar.

Yace:

"Har yanzu Gwamnati na shirin kara farashin mai da sunan cire tallafi. Mu dai mun yanke shawara kuma mun fada mata cewa wahalan da yan Najeriya suka sha ya yi haka kuma ba zamu yarda a kara azabtar da su ta hanyar kara farashin mai da lantarki ba."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa kan masu haike wa yara

"A zaman da mukayi ranar 15 da 17 da Disamba, 2021, kungiyar kwadago ta yanke shawarar zanga-zangan shirin kara farashin mai da gwamnati ke yi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An shirya zanga-zangar ranar 27 ga Junairu, 2022 a dukkan jihohin Najeriya. A ranar 1 ga Febrairu 2022 kuma za'ayi na kasa gaba daya a Abuja."

Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, Kungiyar kwadago a sakon sabon shekara
Zamu rikirkita Najeriya idan aka kara farashin fetur da lantarki, Kungiyar kwadago a sakon sabon shekara
Asali: Twitter

Har yanzu wasu jihohi bakwai basu biyan mafi karancin albashi

Ayuba Wabba ya lissafa jihar Zamfara, Taraba, Benue, Kogi, Cross Rivers, Abia da Imo matsayin jihohin da har yanzu basu biyan ma'aikata mafi karancin albashin N30,000.

A cewarsa, tun ranar 18 ga Afrilu, 2019 ya wajaba a rika biyan ma'aikata mafi karancin albashi.

Ya umurci ma'aikatan wadannan jihohi su fara yajin aiki da zanga-zanga

Asali: Legit.ng

Online view pixel