Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Sake Tsawaita Wa’adin Hada Layukan Waya Da Lambar NIN

Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Sake Tsawaita Wa’adin Hada Layukan Waya Da Lambar NIN

  • Kuma dai, gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake kara wa'adin hada layukan waya da lambar NIN ga yan Najeriya da ba su yi rajistan layinsu ba
  • Wannan sabon karin wa'adin ya faru ne sakamakon rokonn alfarma da masu ruwa da tsaki suka yi ciki har da yan Najeriya da yan Najeriya mazauna kasashen ketare
  • A cewar hukumar sadarwa ta kasa, NCC, ana sa ran za a cigaba da hada lambar wayar da lambar NIN har zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2022

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake tsawaita lokacin cigaba da hada layukan wayoyin salula da lambar zama dan kasa NIN da watanni uku.

The Cable ta ruwaito cewa an tsawaita cigaba da yin rajistar har ranar 31 ga watan Maris din 2022.

Kara karanta wannan

Manyan Hafsoshin Sojin ruwa na hada kai da barayi wajen sace man fetur, Hukumar Navy

Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Sake Tsawaita Wa’adin Hada Layukan Waya Da Lambar NIN
Yanzu-Yanzu: Gwamnati Ta Sake Tsawaita Wa’adin Hada Layukan Waya Da Lambar NIN
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Isa Pantami, Ministan Harkokin Sadarwa da tattalin arzikin zamani ne ya sanar da wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a ranar Juma'a, 31 ga watan Disambar 2021.

Sanarwar tana dauke ne tare da sa hannun Ikechukwu Adinde, direktan sashin hulda da jama'a na hukumar sadarwa ta Najeriya, NCC, da Kayode Adegoke, shugaban sashin sadarwa na hukumar yin rajistan katin dan kasa, NIMC.

Ministan ya ce an tsawaita wa'adin ne saboda bukatar da masu ruwa da tsaki da yan Najeriya suka nema har ma da yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Kimanin yan Najeriya miliyan 71 ne suka yi rajistan NIN

Pantami ya ce a kalla yan Najeriya miliyann 71 ne suka yi rajista tare da samun lambar NIN, cikinsu kuma mafi yawanci suna da layukan waya biyu zuwa uku da suka hada da lambarsu ta NIN.

Kara karanta wannan

Zamu horad da karin matasa sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani, Pantami

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"A zuwa ranar 30 ga watan Disambar 2021, hukumar NIMC ta yi wa mutane miliyan 71 rajistan lambar NIN sannan ta kafa cibiyoyin rajistan fiye da 14,000 a sassan kasar.
"Bugu da kari, hukumar NIMC ta kafa cibiyoyin yin rajistan a kasashe fiye da 31 na duniya domin yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje.
"Adadin na mutane fiye da miliyan 71 da suka samu lambar ta NIN cikin kankanin lokaci, mafi yawansu masu layuka uku ko hudu, ya nuna jajircewa na gwamnatin tarayya, da mazauna kasar kuma wannan abin yabo ne.
"Bisa bukata daga masu ruwa da tsaki, ciki har da yan Najeriya da Yan Najeriya da ke kasashen waje, Gwamnatin Tarayya ta tsawaita cigaba da hada NIN da Layin waya zuwa ranar 31 ga watan Maris na 2022."

Sanarwar ya cigaba da cewa wannan karin zai bawa gwamnatin tarayya damar yi wa mutane rajistan a wurare masu muhimmanci kamar kauyuka, kasashen waje, makarantu, asibitoci, wuraren ibada da yiwa sauran yan kasa rajista.

Kara karanta wannan

Babban Magana: 'Yan Ta'adda Dagar Kasar Waje Na Shirin Kai Hari a Abuja

Ministan na sadarwa ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su dage su hada lambobin su na NIN da layukan wayoyinsu cikin wannan wa'adin.

Ya kuma jadada cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da tallafawa hukumar NCC da NIMC don ganin sun cimma wannan maufar tasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel