Zamu horad da karin matasa sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani, Pantami

Zamu horad da karin matasa sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani, Pantami

  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani yace matasan Najeriya za su amfana da haɗin guiwar FG da kamfanin Huawei Nigeria
  • Farfesa Isa Pantami yace yarjejeniyar da aka sawa hannu zata horad da karin matasa 30,000 ilimin fasahar zamani
  • A cewar shugaban Huawei Nigeria, Liuyan Trevor, a shirye suke su bada gudummuwa a bangaren inganta fasaha a Najeriya

Abuja - Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace za'a horad da karin matasan Najeriya sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani.

The Nation ta rahoto cewa wannan na ɗaya daga cikin amfanar da yan Najeriya za su yi da hadin guiwar ma'aikatar sadarwa da kamfanin Huawei Technologies Nigeria.

Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin ɓangarorin biyu, da nufin ƙara inganta ilimin zamani (Digital Literacy) ga yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan Shi'a sun halarci bikin Kirismeti tare da mabiya addinin Kirista a Zaria

Farfesa Pantami
Zamu horad da karin matasa sama da 30,000 kan ilimin fasahar zamani, Pantami Hoto: Dr Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Kazalika kamfanin ya yi amfani da taron wajen mika kyaututtuka ga waɗan da suka samu nasara a zango na karshe a gasar Huawei.

Pantami yace:

"Yarjejeniyar da FG ta sa wa hannu ta ma'aikatar sadarwa, a ɗaya hannun kuma kamfanin Huawei Nigeria, zai maida hankali ne wajen kara inganta kwarewar yan Najeriya."
"Musamman sabida yadda duniya ke canza wa a yanzu, akwai bukatar dalibai su samu kwarewar fasaha da za su iya yin abu a aikace .
"Shiyasa mukai tunanin samar da MoU domin ganin, a ɓangaren kokarin da kamfanin Huawei ke yi, sun tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan."

A shirye mukule mu tallafawa Najeriya

Shugaban Huawei Najeriya, Liuyan Trevor, ya bayyana cewa a shirye suke su taimaka wajen daga tattalin arzikin zamani a Najeriya ta hanyar ilimantar da matasan Najeriya su kware a bangaren fasaha.

Kara karanta wannan

Coca Cola ta kaddamar da 'Project EQUIP' a Kano: Ga Muhimman abubuwa 3 da shirin zai mayar da hankali a kai

Ya kara da cewa za su yi iyakar bakin kokarin su wajen gina duniyar fasaha ta hanyar inganta sashin tattalin arzikin zamani, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.

A wani labarin na daban kuma Shahararren Malamin addinin musulunci a jihar Kano ya fice daga jam'iyyar APC

Fitaccen malamin addinin Islama a Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel, ya rubuta takardan murabus daga mamban APC.

Shehin Malamin yace ya jima yana son fita daga jam'iyyar amma majalisar malamai na shiga tsakani ta sasanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262