Da duminsa: Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan Kasafin Kudin N17.127 Trillion na 2022

Da duminsa: Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan Kasafin Kudin N17.127 Trillion na 2022

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan daftarin kasafin kudin Najeriya na shekarar 2022 da za'a shiga.

Shugaban kasa ya rattafa hannun da safiyar Alhamis, 31 ga Disamba, 2021, ranar karshen shekara.

Rattafa hannun Shugaba Buhari ya biyo bayan amincewa da kasafin kudin da gyare-gyaren da majalisar dattawa da ta wakilai suka yi.

Wadanda suka shaida rattafa hannun sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Rattafa hannun na nufin cewa daftarin kudin ya zama doka kuma lissafe-lissafen kudin da akayi za'a kashe a sabuwar shekara.

Da duminsa: Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan Kasafin Kudin 2022
Da duminsa: Shugaba Buhari ya rattafa hannu kan Kasafin Kudin 2022
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan Majalisar sun amince da Kasafin Kudin 2022, sun kara N700bn

Kara karanta wannan

Manyan Hafsoshin Sojin ruwa na hada kai da barayi wajen sace man fetur, Hukumar Navy

Za ku tuna cewa Majalisar wakilan tarayya a ranar Talata, 21 ga Disamba 2021, da kuma majalisar dattawa ranar Laraba sun amince da daftarin kasafin kudin 2022 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabata mata a watan Oktoba.

Maimakon N16.39tr da Buhari ya gabatar, yan majalisan sun kara sama da bilyan 700 kai zuwa N17.126 trillion.

ChannelsTV ta ruwaito cewa majalisar ta kara N400bn wa ma'aikatu irinsu INEC, Majalisar dokoki da ma'aikatar tallafi da jin kai, dss.

Majalisa kuma ta kara kiyasin farashin danyen mai daga $57/ganga zuwa $62/ganga.

Yan majalisan kuma sun ce hukumar EFCC da NFIU su rika amfani da kashi 10% na kudaden da suka kwato don karfafa yaki da rashawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel