NDLEA ta yi ram da jami'an bogi 3 dauke da 427kg na miyagun kwayoyi a Borno da Abuja

NDLEA ta yi ram da jami'an bogi 3 dauke da 427kg na miyagun kwayoyi a Borno da Abuja

  • Jami'an hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun cafke wasu jami'an tsaro 3 na bogi dauke da miyagun kwayoyi
  • Daya ya bayyana sanye da kayan sojoji inda ya ke tuka motarsa dauke da kwayoyin domin gujewa jami'an tsaron kan hanya
  • Jimillar nauyin miyagun kwayoyin da aka cafke jami'an tsaron bogin da su sun kai 427kg a jihohin Borno da Abuja

FCT, Abuja - Jami'an hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi na kasa, NDLEA, sun damke wasu masu safarar miyagun kwayoyi 3 da ke sanye da kayan jami'an tsaro domin gujewa bincike.

Jami'an tsaron na bogi an kama su dauke da 427kg na miyagun kwayoyi a jihar Borno da babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta yi kaca-kaca da wasu kasuwanni biyu a jihar Sokoto, ta kone shaguna

Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis, ya ce Yakubu Kotri, wanda yayi basaja kamar jami'in soja, ya shiga hannu a ranar Laraba da ta gabata yayin da yake tuka motarsa kirar Golf dankare da wiwi mai nauyin 208kg kan hanyarsa ta zuwa Bama a jihar Borno.

NDLEA ta yi ram da jami'an bogi 3 dauke da 427kg na miyagun kwayoyi a Borno da Abuja
NDLEA ta yi ram da jami'an bogi 3 dauke da 427kg na miyagun kwayoyi a Borno da Abuja. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Babafemi ya ce, wani wanda ake zargi mai suna Salisu Mohammed ya kawata kansa da kayan jami'an tsaron kan titi domin safarar Tramadol zuwa Bama, kuma jami'an NDLEA sun yi ram da shi yayin da suka fita sintiri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk da hotunan wadanda aka kama da kayan jami'an tsaron suna ta yawo a kafafen sada zumunta tun ranar Laraba, hukumar ta barranta kanta daga hakan saboda ba a tabbatar da cewa wadanda ake zargin sojoji bane," takardar tace.

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

Har ila yau, a ranar Laraba jami'an hukumar sun cafke Dada Adekunle tare da wani abokin ta'asar sa mai shekaru sittin a duniya mai suna Usman Isa a yankin Abaji da ke FCT da wiwi mai nauyin 15.843kg, yayin da aka kwace 20kg na wiwi daga wani Alfred Aminu wanda aka damke a Gwagwalada.

NDLEA ta damke 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wasu 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa miyagun 'yan ta'adda kwayoyi a Najeriya.

An cafkesu ne a makon da ya gabata a jihohin Taraba da kuma Nijar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana hakan a Abuja yayin da shi tare da kungiyarsa suka ziyarci ministan yada labarai da al'adu na kasar nan, Lai Mohammed.

Kara karanta wannan

Kwastam ta yi babban kamu, ta kame kwantena makare da tramadol na biliyoyi

Marwa yace hukumar tayi nasarar damke masu safarar kwayoyi 2,175, an kwace kilogram 2,050,765.33 na miyagun kwayoyi tare da kwace magunguna da zasu kai darajar N75 biliyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel