Ba zata sabu ba: Shugabanni a Adamawa sun ki amincewa da batun karin gundumomi a jihar

Ba zata sabu ba: Shugabanni a Adamawa sun ki amincewa da batun karin gundumomi a jihar

  • Shugabannin Jimeta a Adamawa sun nuna rashin amincewarsu a kan batun karin gundumomi a jihar
  • Shugabannin karkashin jagorancin tsohon kakakin Majalisar jihar Adamawa, Muhammad Turaki, sun gabatar da matsayarsu ga majalisar dokokin jihar
  • Sai dai kuma, Hammantukur Yettisuri, shugaban masu rinjaye a majalisar jihar, ya ce gwamnatin jihar bata da hannu a cikin lamarin

Adamawa - Shugabannin al’umma a Jimeta sun yi watsi da bukatar kafa sabbin gundumomi biyu a garin Adamawa.

Tawagarsu mai karfi karkashin jagorancin tsohon kakakin Majalisar jihar Adamawa, Muhammad Turaki, sun gabatar da matsayarsu .

Sun gabatar da matsayar tasu ne ga kwamitin wucin-gadi na majalisar kan kafa sabbin gundumomi a Yola a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ba zata sabu ba: Shugabanni a Adamawa sun ki amincewa da batun karin gundumomi a jihar
Ba zata sabu ba: Shugabanni a Adamawa sun ki amincewa da batun karin gundumomi a jihar Hoto: The Cable
Asali: UGC

Turaki ya bayyana cewa kafa sabbin gundumomi rashin tunani ne ta fuskacin tattalin arziki duba ga cewar gundumomin da ke kasa sun kasa biyan albashi tsawon watanni da dama.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A nashi bangaren, Usman Wakili, tsohon hadimin tsohon Gwamna Murtala Nyako, ya bayyana cewa yunkurin bai samu goyon bayan mafi akasarin mutanen Jimeta ba.

Daily Trust ta kuma rahoto cewa a martaninsa, shugaban kwamitin, Hammantukur Yettisuri, wanda shine Shugaban masu rinjaye a majalisar jihar, ya ba shugabannin tabbacin cewa Za su yi adalci ga bukatarsu kuma za su duba korafinsu.

Sai dai kuma, ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar bata da hannu a yunkurin na kafa sabbin gundumomi.

A wani labari na daban, sabon karamin ministan ayyuka da gine-gine, Mu'azu Sambo, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki hanyar da ta dace domin bunkasa ababen more rayuwa a kasar.

Ya bayyana hakan yayin da ya kama aiki a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, sannan ya samu tarba daga sakataren din-din-din, Babangida Hussaini, da ma'aikatan ma'aikatar.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai ya ba da sandar sarauta ga basaraken gargajiya na garin Lere

Sambo ya tabbatar da cewa ’yan Najeriya, wadanda ke shakka a kan iyawar Buhari za su gane muhimmancinsa ne bayan gwamnatinsa ta kare, jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel