Gwamnati na neman aron kudi, abin da ake bin Najeriya zai kai N50tr kafin Buhari ya sauka

Gwamnati na neman aron kudi, abin da ake bin Najeriya zai kai N50tr kafin Buhari ya sauka

  • Gwamnatin Tarayya tayi tsarin da za ta karbo bashin akalla Naira Tiriliyan nan da shekara hudu
  • Idan aka ci wadannan bashin kudi, zai zama ana bin Gwamnatin Najeriya Naira tiriliyan 50.2 a 2023
  • Alkaluman Ofishin DMO ya nuna kawo yanzu kudin da ake bin kasar nan bashi ya kusa kai N40tr

Abuja – Wani rahoto na jaridar Punch ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta na kokarin kai adadin bashin da ake bin Najeriya zuwa Naira tiriliyan 50.22.

Tsarin National Development Plan na shekarar 2021 zuwa 2025 ya nuna cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da karbon aron kudi daga hannun bankuna.

Rahoton yace tsakanin 2021 zuwa 2023, lokacin da Muhammadu Buhari zai bar mulki, gwamnatinsa ta na da burin cin bashin Naira tiriliyan 12.

Sai zuwa shekarar 2025, gwamnatin tarayya ta ke lissafin cewa za ta rage karbo aron kudi.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa

Jaridar The Street Journal tace gwamnatin tarayya za ta bukaci kudi domin a iya aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kasar wanda za su ci N348tn.

Gwamnati
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda za a rika cin bashi duk shekara

A shekarar 2021 gwamnati na harin bashin ya kai N39.59tn, sai N46.63tn a 2022, zuwa N50.22tn a 2023, da N50.53tn a 2024, a shekarar 2025 sai ya koma N45.96tn.

Kashi 45% na bashin zai fito daga bankunan gida, haka zalika za a karbo aron 45% na kudin daga ketare. Gwamnati za ta kawo tsare-tsaren da za a samu ragowar.

A tsawon wannan lokaci da ake tsari, za a kashe kusan Naira tiriliyan 50 a ayyukan more rayuwa.

Ra’ayin masana tattalin arziki

Wani masanin tattalin arziki, Omosuyi Temitope, ya bayyana cewa duk da bashin da ake ci ya na ta kara yawa, akwai bukatar gwamnati ta nemo aron kudin.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun kara Naira Biliyan 720 a kundin kasafi kudi, Najeriya za ta kashe N17.12tr a 2022

Shi kuma Farfesa Sheriffdeen Tella wanda yake karantar da ilmin tattalin arziki a jami’ar Ago-Iwoye, yace ya kamata a nemi wasu hanyoyin samun kudin.

Shi ma Dr. Muda Yusuf ya na ganin bashin da ake karbowa na nema ya fara yi wa gwamnati yawa.

Bashin da ke wuyan Najeriya ya kai N38tr

Idan za a tuna, a farkon shekarar nan ne Patience Oniha ta ce basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin jihohin yanzu ya kai N33.63tr.

Ofishin DMO ya tabbatar da cewa bashin da ke kan gwamnatin Najeriya a karshen 2021 ya kai N38trn bayan an karbo aron N2.540tn a cikin watanni uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel