Sanatoci sun kara Naira Biliyan 720 a kundin kasafi kudi, Najeriya za ta kashe N17.12tr a 2022

Sanatoci sun kara Naira Biliyan 720 a kundin kasafi kudi, Najeriya za ta kashe N17.12tr a 2022

  • Majalisar dattawa ta amince da kundin kasafin kudin da aka gabatar mata na shekara mai zuwa
  • Sai dai Sanatoci sun kara kimanin Naira biliyan 720 akan abin da Muhammadu Buhari ya kawo
  • Daga N16.4tr da aka yi lissafi, Majalisa ta kara kasafin kudin gwamnatin Najeriya zuwa N17.4tr

FCT, Abuja - A ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, majalisar dattawa ta amince gwamnatin Najeriya ta kashe N17,126,873,917,692 a shekarar badi.

Jaridar Tribune tace majalisar dattawan ta dauki wannan matsaya ne kwana guda bayan ‘yan majalisar wakilai sun amince kasafin kudin a yadda ya zo.

A daidai lokacin da majalisar wakilan tarayya ba ta kara komai a kan adadin kundin kasafin kudin kasar ba, Sanatoci sun kara kimanin Naira biliyan 720.

Abin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar shi ne N16.4tr. Yanzu abin da za a kai masa ya sa hannu shi N17.12, an samu karin har N700bn.

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

‘Yan majalisar kasar sun kara kudin da aka yi gangar danyen man Najeriya daga $57 zuwa $62, ganin cewa danyen mai ya kara kudi a kasuwannin Duniya.

Premium Times tace ana sa ran a duk rana, Najeriya za ta hango ganguna 1.86 na danyen mai.

Sanatoci
Shugaban Majalisar Dattawa, Hoto: @NgrSenate
Asali: Twitter

Shugaban kwamiti ya gabatar da rahoto

Sanatoci sin amince da kundin kasafin kudin shekarar 2022 bayan sauraron rahoto da shawarwarin da shugaban kwamitin, Sanata Barau Jibrin ya gabatar.

Da yake jawabi Sanatan na yankin Kano ta Arewa, yace sun bada shawarar a ware N869.6bn na wadanda ake tura masu kudinsu dabam daga asusun tarayya na kasa.

Rahoton yace Sanata Barau Jibrin yace an kara gibin da ke cikin kasafin kudin domin a iya daukar nauyin wasu muhimman abubuwa da ba yi la’akari da su ba.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun shiga ganawar sirri kan sabon kundin zabe 2021 da Buhari ya ki sa hannu

Ga yadda aka yi lissafin majalisar dattawan yake:

Masu cin gashin kan su – N869,667,187,542

Biyan bashi – N3,879,952,981,550

Albashi da sauran hidindimun yau da gobe – N6,909,849,788,737

Ayyukan more rayuwa – N5,467,403,959,863

Karin ya shafi ayyukan more rayuwa da za a gudanar da kason ma’aikatun gwamnatin tarayya irinsu INEC, NPC, ofishin NSA da kason majalisa na ayyukan mazabu.

Kudirin gyaran zabe ya sha ruwa?

A jiya da yamma ne ake jin cewa Gwamnonin Jihohi sun jagula yunkurin wasu Sanatocin adawa na shigo da kudirin gyaran zabe ta bayan fage a Majalisar Tarayya.

Maganar ta shiririce kwatsam bayan Sanatoci sun samu kuri’a kusan 80 da za su yi watsi da matakin da Shugaban kasa ya dauka bayan sa bakin gwamnonin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel