Bashin da ake bin Najeriya ya kai N33.63 Trillion, Ofishin manajin basussuka DMO

Bashin da ake bin Najeriya ya kai N33.63 Trillion, Ofishin manajin basussuka DMO

- Biyo bayan maganar buga N60bn don rabawa gwamnoni, DMO ta bayyana bashin da ake bin Najeriya

- Gwamnan CBN ya ce an buga kudin ne don baiwa gwamnoni rance

Dirakta Janar na Ofishin manajin basussukan Najeriya DMO, Patience Oniha, ta ce basussukan da ake bin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin yanzu ya kai N33.63 trillion.

A jawaban da ta saki a shafin sadarwanta na Tuwita, Oniha ta ce jita-jitan da ake yadawa kan adadin bashin da ake bin Najeriya yasa ta wallafa jerin basussuka.

A cewarta, "yana da muhimmanci in fayyace cewa wannan bashin na gwamnatin tarayya ne, birnin tarayya, da jihohin Najeriya 36,"

"Bashin ba na gwamnatin tarayya bane kadai, gwamnonin jihohi da birnin tarayya na karban bashi."

"A bangaren gwamnatin tarayya, adadin bashin da aka karba ya karu ne saboda fadin farashin danyen mai a 2015."

"Amma a kasafin kudin 2018 zuwa 2020, adadin basussukan sun ragu."

"Abin takaici, illar annobar COVID-19 kan kudin shiga ya sabbaba tashin basussukan."

Za ku tuna cewa a karshen shekarar 2020, DMO ta ce bashin da ake bin Najeriya ya kai N32.9tr.

KU KARANTA: Jerin jihohi 5 da suka fi aiwatarwa al'ummarsu manyan ayyuka na kasafin kudi, Kaduna ce ta farko

Bashin da ake bin Najeriya ya kai N33.63 Trillion, Ofishin manajin basussuka DMO
Bashin da ake bin Najeriya ya kai N33.63 Trillion, Ofishin manajin basussuka DMO
Asali: Twitter

DUBA NAN: Ba ni na raba shinkafa a Kano ba amma ina godiya ga wadanda sukayi, Tinubu

A bangare guda, Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya yi fashin baki kan musayar kalaman dake faruwa tsakanin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da Ministar Kudi, Zainab Ahmed.

A makon jiya, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin rashin kudi saboda sai da aka buga wasu biliyoyi a watan Maris aka rabawa jihohi.

Amma a ranar Laraba Gwamnatin tarayya ta siffanta kalaman gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na cewa an buga kudi N60bn don rabawa gwamnoni a matsayin karya maras tushe da asali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng