Zamfara: Mutane sun tsere daga gidajensu bayan 'yan bindiga sun kashe mutum 10 sun sace mata 33

Zamfara: Mutane sun tsere daga gidajensu bayan 'yan bindiga sun kashe mutum 10 sun sace mata 33

  • ‘Yan bindiga sun halaka mutane 10 sannan sun yi garkuwa da mata 33 a kauyuku bakwai da ke karkashin karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara
  • An samu bayanai akan yadda mazauna kauyukun su ka dinga guduwa Gusau don neman tsira saboda babu jami’an tsaron da zasu kai musu dauki daga ‘yan bindigan
  • Mazauna yankin sun bayyana yadda ‘yan bindigan su ka shiga kauyukan a baburansu a ranar Lahadi inda su ka dinga sata a shaguna da gidaje

Jihar Zamfara - ‘Yan bindiga sun halaka mutane 10 sannan sun yi garkuwa da mata 33 daga kauyuku bakwai da ke karkashin karamar hukumar Gusau a jihar, The Punch ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda mazaunan su ka tsere zuwa cikin garin Gusau don neman tsira saboda babu jami’an tsaro a kauyakun da za su dakatar da ‘yan bindigan daga farmakin da su ke kai musu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun hallaka mutane sun sace mata 33

Zamfara: Mutane sun tsere daga gidajensu bayan 'yan bindiga sun kashe mutum 10 sun sace mata 33
Mutanen gari sun tsere bayan 'yan bindiga sun kashe 10 sun yi garkuwa da 33 a Zamfara. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mazaunin yankin, Malam Shehu Kura, wanda ya tsere zuwa wuraren Damba a Gusau ya shaida wa wakilin The Punch cewa ‘yan bindigan sun isa kauyakun ranar Lahadi a baburansu inda su ka dinga sace-sace a gidaje da shaguna.

A cewarsa ‘yan bindigan sun kwashe sa’o’i da dama su na ta’addanci a kauyakun guda bakwai ba tare da jami’an tsaro sun dakatar da su ba.

Sun dinga bincike gida-gida

A cewar Kura:

“Sun kwashe sa’o’i da dama a wurarenmu, inda su ka yi bincike gida-gida su ka dinga neman kayan abinci da sauran abubuwa masu daraja.”

Wani ganau ya shaida cewa ‘yan bindigan sun sace mata 33 kuma sun yashe kayan abinci da yawa.

A cewarsa:

“Sun yi garkuwa da mata 10 daga kauyen Kura, 9 daga Bayawuri, 7 daga Gana da kuma wasu 7 daga Doma.”

Kara karanta wannan

Babu kanta yayin da ‘Yan bindiga suka dauke Mai daki, 'ya ‘yan ‘Dan Sanda a jajibirin Kirismeti

Mazaunan sun bayyana yadda a take a wurin ‘yan bindigan su ka halaka mutane 10 yayin da suke kokarin guduwa kuma wasu da dama sun samu miyagun raunuka.

Duk da matsanancin sanyin da ake yi a waje suke kwana don rashin yadda zasu yi

Kura ya bayyana yadda mutanen kauyaku bakwai din suka dinga tserewa garin Gusau kuma ya ce yawancinsu a takure suke saboda rashin matsuguni.

A cewarsa:

“Da yawanmu a waje muke kwana ko kuma a tsakar anguwanni duk da tsananin sanyin da ake fama da shi saboda bamu da wani zabin.”

Kura ya bukaci tallafin hukuma

Ya roki hukuma da ta taimakesu inda yace yawancin wadanda lamarin ya shafa mata ne da yara.

Ba a samu damar jin ta bakin kwamishinan labaran jihar, Alhaji Ibrahim Dosara, ba don jin tsokacinsa dangane da lamarin.

Sai dai kwamishinan ya shaida wa BBC Hausa cewa harin kauyen Geba kadai ya sani, a cewarsa an tura jami’an tsaro kauyen.

Kara karanta wannan

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel