Zulum ga 'yan soshiyal midiya: Ku daina kamanta aiki na da na wasu gwamnoni, cin zarafi ne

Zulum ga 'yan soshiyal midiya: Ku daina kamanta aiki na da na wasu gwamnoni, cin zarafi ne

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna godiyarsa ga masoyansa na soshiyal midiya
  • Gwamna Zulum ya bukaci masoyansa da su daina kamanta nasarorinsa da ayyukansa da na sauran gwamnoni
  • Zulum ya ce hakan cin mutunci ne kuma kowacce gwamnati ta na da abinda ta bai wa fifiko wurin ingantawa

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna godiyarsa ga masoyansa na soshiyal midiya.

Sai dai Zulum ya roki wasu masoyansa da su daina hada nasarorinsa da na sauran gwamnonin don kowa da irin matsalar da ke gabansa, Daily Trust ta ruwaito.

Zulum ga 'yan soshiyal midiya: Ku daina kamanta aiki na da na wasu gwamnoni, cin zarafi ne
Zulum ga 'yan soshiyal midiya: Ku daina kamanta aiki na da na wasu gwamnoni, cin zarafi ne. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mai bai wa gwamnan shawarwari a harkar hulda da jama’a, Malam Isa Gusau, ya sanar da hakan ta wata takarda ta ranar Litinin.

Kara karanta wannan

An dakatar da Malami daga karantarwa saboda ya na caccakar Gwamnan APC a Facebook

Kamar yadda takardar ta bayyana:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yayin da nake godiya akan masoyana na soshiyal midiya, amma an tura mana wasu sakwanni cikin ‘yan kwanakin nan akan ayyukan jihar Borno da ake hadawa da na wasu jihohin da nufin cin zarafi.
"Ba na jin dadi idan naga ana hada ayyuka na da na wasu gwamnonin da sunan cin mutunci musamman ga wadanda su ke amfani da shafuka da ke da alaka da mu .
“Gaskiya hadakar ba ta mana dadi saboda ba gasa muke yi ba. Maganar gaskiya shine ko wacce gwamnatin jiha daga jihohi 36 ta na da na ta matsalar da abinda tafi mayar da hankali akai.
“Ga gwamnatin jihar Borno, mun dage da ganin mun taso da jihar sakamakon rikicin shekaru 12 da jihar ta fuskanta wanda ya janyo kashe-kashen mutane sannan wasu mutane fiye da miliyan 2 suka rasa gidajensu.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Daga rahoton bankin duniya akan arewa maso yamma, a jihar Borno mutane sun rasa gidaje 956,453, hakan kashi 30% ne na yawan gidajen da ke fadin jihar, duk saboda ‘yan ta’adda.

“Sannan an tafka asara a gine-ginen cikin gari guda 665 har da ma’aikatu, na kananun hukumomi, gidajen gyaran hali, ofisoshin ‘yan sanda da ofisoshin wutar lantarki da ke fadin jihar Borno. Azuzuwa 5,334 da sauran bangarori na cikin makarantu inda aka lalata makarantun firamare 512, makarantun sakandare 38 da wasu jami’o’in da ke jihar.

Asibitoci 201, mafi yawa na anguwanni da wasu manyan asibitoci. ‘Yan ta’adda sun lalata ofisoshin wutar lantarki 726 da hanyoyin ruwa guda 1,630 har da tuka-tuka.

“Don haka ci gaban jihar Borno ba na gasa bane, amma kowa akwai kalubalen da yake fuskanta. Kowacce jiha akwai abubuwan da take bukata don haka kowanne gwamna akwai salon da zai bi don yi wa jiharsa aiki.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

"Mu dake jihar Borno mun fi bukatar yin aiki cikin sauri don kawo garanbawul ga matsalolin da muke fuskanta don haka bai dace a dinga hada mu da sauran jihohi ba,” a cewar Farfesa Zulum.

Gusau ya kara a cikin takardar inda yace Zulum ya roki duk wani masoyinsa na gaskiya da ya guji zagin wani shugaba yana hada nasararsa da ta jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri

A wani labari na daban, 'yan ta'addan Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin sama da ke yankin Ngomari a Maiduguri yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin sauka a birnin yau Alhamis.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, daya da cikin makaman masu linzami ya tsallake har zuwa Ajilari, kusa da filin jiragen sama na Maiduguri inda sansanin sojoji ya ke.

Majiyoyi sun ce mutum daya ya rasa ransa a Ngomari yayin da wasu suka samu raunika a yankin Ajilari. Alamu suna nuna cewa, maharan sun daidaita tare da saitar filin saukar jiragen saman ne saboda makaman sun sauka 10:45 na safe, mintoci kadan kafin isar Buhari birnin.

Kara karanta wannan

Masari da Ganduje: Lokaci ya yi da za mu daina wannan wasan, mu yaki 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel