An dakatar da Malami daga karantarwa saboda ya na caccakar Gwamnan APC a Facebook

An dakatar da Malami daga karantarwa saboda ya na caccakar Gwamnan APC a Facebook

Ma’aikatar ilmi ta Osun ta dakatar da wani malamin sakandare daga aiki saboda ya na sukar gwamna

Ana zargin malamin da sukar gwamna Gboyega Oyetola wanda hakan ya sabawa aikin gwamnati

Ganin yawan sukar APC da malamin yake yi a shafin Facebook, sai abokan aikinsa suka kai karar shi

Osun - Gwamnatin jihar Osun ta dakatar da wani malamin sakandare, Akiyemi Philip saboda ya zagi gwamna Gboyega Oyetola a shafin sada zumunta.

Jaridar Premium Times tace ana zargin Akiyemi Philip da caccakar Mai girma gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola a kan rigimar da ake yi a APC.

Mista Philip ya na koyarwa ne makarantar Masifa Community Grammar School a yankin Ejigbo. Abokan aikinsa ne suka kai kararsa gaban mahukunta.

Me Akiyemi Philip yake fada a Facebook?

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Da jaridar ta bibiyi shafin wannan malami na Facebook, sai aka ga cewa ya na yawan sukar bangaren Gboyega Oyetola, yana goyon-bayan ‘yan taware.

"Elegbeleye da mutanensa da suka gudanar da zaben shugabannin APC ne aka zaba domin su gudanar da zaben fitar da gwani na APC. Sai Iwaloye 2022."
“Ka da a ba wanda ya ci amana tazarce. Ya kamata yakin da aka yi tsakanin 2016 zuwa 2020 ya zama darasi ga wadanda suke kan mulki ko masu barin gado.”
- Akiyemi Philip
Malamin Osun
Gwamna Oyetola da Akiyemi Philip Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Gwamnati ta dauki mataki a kan malamin sakandaren

A watan Disamban nan ne ma’aikatar ilmi ta jihar Osun ta aikawa malamin makarantar sammaci domin jin dalilin da ya sa yake yi wa gwamnati adawa a fili.

Kamar yadda Punch ta bayyana, da yake kare kansa, Phillip yace bai taba zagin gwamnan ba, kuma ya na cikin manyan masu biyayya ga gwamna Oyetola.

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

Ban taba zagin Gwamna ba – Akiyemi Philip

Malamin yace ya na cikin wadanda suka tsayawa gwamnati a matsayin shaidunta a lokacin da APC ta ke ta shari’a da Sanata Ademola Adeleke a kotun zabe.

Duk da bayanin da ya yi, ma’aikatar ilmi ba ta gamsu ba. A karshe ofishin ma’aikatar ilmi ta Osun ta yamma ta dakatar da malamin har sai ranar da aka neme shi.

Rigimar cikin gidan APC a Osun

A halin yanzu rikicin cikin gida ya barke a jam’iyya a dalilin sabanin da aka samu tsakanin tsohon gwamna, Ogbeni Rauf Aregbesola da magajinssa, Oyetola.

An ji ba a ga maciji tsakanin Adegboyega Oyetola da Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola. Sannan akwai ‘yar tsama tsakanin gwamna da Hon. Yusuf Lassun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel