Okorocha ya fadi mutane 2 da ke da hannu wajen ba ‘Yan Sanda umarnin cafke surukinsa

Okorocha ya fadi mutane 2 da ke da hannu wajen ba ‘Yan Sanda umarnin cafke surukinsa

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya sake yin kaca-kaca da Gwamna Hope Uzodinma
  • Sanata Rochas Okorocha yace Hope Uzodinma ne ya sa IGP ya bada umarni a cafke Uche Nwosu
  • Okorocha yake cewa ‘Yan Sanda sun shiga har coci sun kama surukinsa ne saboda ayi masa sharri

Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya zargi shugaban ‘yan sanda na kasa da bada umarnin a kama surukinsa, Uche Nwosu a coci.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Rochas Okorocha yana cewa Hope Uzodimma ne ya yaudari Sufetan ‘yan sanda ya yi wannan aiki a lokacin da ake yin ibada.

Kamar yadda jaridar ta rahoto, Rochas Okorocha ya bayyana wannen ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a gidansa da ke garin Owerri, jihar Imo.

Kara karanta wannan

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

Tsohon gwamnan yace jami’an ‘yan sandan da suka yi wannan aiki a tsakiyar coci, sun ture mai dakinsa, sannan su ka keta rigar ‘yarsa, Uloma Okorocha.

Okorocha mai wakiltar Imo ta yamma a majalisar dattawa yace gwamnan jihar Imo mai-ci, Sanata Hope Uzodimma ya na kokarin yi wa Nwosu sharri.

Okorocha
Sanatan Imo, Rochas Okorocha Hoto: @RealRochas
Asali: UGC

Abin da Okorocha ya fadawa 'Yan jarida

“Uche Nwosu, mai dakina, da ‘ya ta su na ibada a coci sai aka ji ‘yan sanda sun shigo yayin da ake tsakiyar huduba, suka fara harbe-harbe.”
“Ana haka ne suka jefar da matata a kasa, suka keta rigar jikin ‘diyata. Babu takardun cafke mutum, babu takardar gayyatar ‘yan sanda.”
“Da farko mun dauka satar mutane ne. Mutane da yawa sun samu rauni wajen gudu. Aka jefa Nwosu a mota mai lambar gwamnatin Imo.”

Kara karanta wannan

'Karin bayani: 'Yan sanda sun kama surukin Okorocha a cikin coci a Imo

- Rochas Okorocha

A cewar Okorocha, rundunar ‘yan sandan gidan gwamnati ne suka yi wannan aiki. Kwamishina kuma yace shugaban ‘yan sanda na kasa ya ba shi umarni.

Sanatan ya fadawa ‘yan jarida cewa nema Uzodinma yake yi, ya yi wa Nwosu sharri ko ta wani irin hali, don haka yace akwai bukatar Buhari ya san da haka.

Punch ta rahoto Okorocha yana cewa duk da kwamishinan ‘yan sandan Imo, Rabiu Hussaini yace Nwosu ya na hannunsu, har yanzu bai ji daga gare shi ba.

An dakatar da malami saboda zagin gwamna

Kwanaki aka ji cewa Gwamnatin Osun ta aikawa wani malamin takarda bayan ta ji labarin sukar gwamnan jihar da yake yi a shafinsa na Facebook ya yi yawa.

Da aka tuntubi, Akiyemi Philip mai koyarwa a sakandare, yace bai taba sukar Gwamnan ba, kuma ya na cikin masu goyon bayan gwamna Gboyega Oyetola.

Kara karanta wannan

IGP: Abun tashin hankali ne yadda ISWAP suka iya harba makamai masu linzami a Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel