Yan bindiga sun mamaye dajin Falgore, a kawo dauki: Ganduje ya kai kuka wajen Buhari

Yan bindiga sun mamaye dajin Falgore, a kawo dauki: Ganduje ya kai kuka wajen Buhari

  • Gwamnan Kano ya yi takakkiya zuwa wajen Shugaba Muhammadu Buhari ranar Juma'a ana gobe Kirismeti
  • Ganduje ya bukaci Shugaba Buhari ya gina sansanin horon Sojoji a dajin Falgore saboda kada yan bindiga su mamaye
  • Matsalar tsaro ta zama kaya a wuyan gwamnonin Najeriya musamman na yankin Arewa maso yamma

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, na jihar Kano ya kai kuka fadar mulki dake Aso Villa Abuja wajen Shugaba Muhammadu Buhari bisa lamarin tsaron jiharsa.

Gwamnan ya bayyana yadda yan bindiga suka fara mamaye dajin Falgore dake jihar.

A hirar da yayi da manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da Buhari ranar Juma'a, Ganduje ya bukaci Gwamnatin tarayya ta kawowa Kano dauki.

Ya yi Alla-wadai da yadda matsalar tsaro ta addabi kowa a kasar.

Kara karanta wannan

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

Ganduje ya kai kuka wajen Buhari
Yan bindiga sun mamaye dajin Falgore, a kawo dauki: Ganduje ya kai kuka wajen Buhari Hoto: Ganduje
Asali: Depositphotos

Gwamnan ya bukaci Gwamnatin tarayya ta sake kafa wani sansanin horar da Sojoji a dajin na Falgore wanda ke da iyaka da Kano, Kaduna, Bauchi, da kuma Plateau.

A cewarsa:

"Da farko, na zo ganin Shugaban kasa ne domin yi masa bayani game da lamarin tsaro a Kano."
"Muna bukatan taimakon kowa, musamman gwamnoni da Shugabannin kananan hukumomi. Mun lura cewa dazukanmu ne yan bindiga ke samun matsuguni, nan barayi da batagari ke zama."
"Muna da manyan dazuka biyu, Dajin Falgore, wanda ke iyaka da Kano, Kaduna, Bauchi kuma babu nisa da Plateau."

Asali: Legit.ng

Online view pixel