Lai: Buhari ya samu mulkin Najeriya a yayin da ta ke tsaka da hargitsi da rashin zaman lafiya

Lai: Buhari ya samu mulkin Najeriya a yayin da ta ke tsaka da hargitsi da rashin zaman lafiya

  • Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce duk da kalubale da kasa take fuskanta, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na ci gaba da samun tarin nasarori
  • A cewarsa, duk masu kai hare-haren da aka dauki nauyi da kuma ‘yan adawa na siyasa tare da sauran kalubale, Buhari bai gushe ba sai ayyuka ya ke yi na gani da fadi
  • Ya kara da cewa, babu shakka kuma babu jayayya akan yadda shugaban kasar ya dage wurin bunkasa Najeriya tare da kawo mata ci gaba mara adadi

Abuja - Ministan al’adu da labarai, Alhaji Lai Muhammad ya ce duk da manyan kalubalen da kasar nan ta ke fuskanta ba su hana shugaban kasa Muhammadu Buhari kawo nasarori ba ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce ba ya ga ‘yan bindigan da aka dauki nauyi tare da ‘yan siyasa masu adawa tare da sauran kalubalen da kasa take fuskanta, hakan bai hana Buhari samun nasarori masu yawa ba.

Lai: Buhari ya samu mulkin Najeriya a yayin da ta ke tsaka da hargitsi da rashin zaman lafiya
Lai: Buhari ya samu mulkin Najeriya a yayin da ta ke tsaka da hargitsi da rashin zaman lafiya. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Muhammed ya kara da cewa babu shakka Buhari ya daura Najeriya a mataki na ci gaba da nasarori, Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi wannan furucin ne a Ilorin, jihar Kwara, a wani taro na shagalin zagayowar shekarun Buhari 79 a ranar Asabar.

A cewarsa, “Shugaba Buhari ya shiga matsaloli da dama, amma haka nan ya jajirce akan wannan mummunan halin da kasar nan ta ke fuskanta, sannan ya tsaya don ganin ci gabanta da bunkasarta.
“Duk da halin rashin tsaro da gurguncewar tattalin arziki akan fatarar da kasashe su ka shiga saboda annoba, Buhari ya samu nasarori masu tarin yawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ba zai iya magance matsalar tsaro a shekara mai zuwa ba, inji minista

“Ci gaban da ya samu ba lallai a kula da su yanzu ba, musamman saboda ‘yan adawa, ‘yan bindigan da ake daukar nauyinsu tare da ‘yan siyasa masu burin tura shi kasa amma duk da haka nasarori masu yawa kasar nan ke samu. Kullum ya na kwana da tashi ne da tunanin Najeriya a zuciyarsa.
“Ya yi yaki don hadin kan Najeriya, don haka hakan ya na nuna kaunar da ya ke yi wa Najeriya.
“Duk abinda ke faruwa ya na da dalili. Buhari ya na kula da Najeriya yadda ya dace. Shekarun da ya yi yana soja ya kai kololuwar daukaka sannan fitar da ya ke yi waje ya gogar da shi.”

Ya kara da bayyana yadda mulkin nan ya kankaro wa kasar nan daraja da ci gaba a idon duniya. Inda ya ce Buhari ya cancanci girmamawa da daraja. Don haka Ubangiji ya na da dalilin barin da da rai yayin da mutane da dama su ka mutu.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

Gyara Kimtsi: An nada ministan Buhari, Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi

A wani labari na daban, sarkin Argungun, Mai Martaba Sumaila Mera a ranar Lahadi ya bai wa ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa an yi nadin sarautar a cikin fadar sarkin Argungun da ke jihar Kebbi duk daga cikin jerin shagalin ranar shakatawa da za a yi a Birnin Kebbi ranar Litinin.

A yayin jawabi wurin bikin, sarkin ya ce an bai wa ministan wannan sarautar ne saboda kwazonsa wurin karfafa kyawawan tsarin al'adun Najeriya a gida da waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel