Shatu Garko: Gasar Sarauniyar Kyau Tamkar Shirin BBNaija Ne, MURIC Ta Goyi Bayan Hisbah

Shatu Garko: Gasar Sarauniyar Kyau Tamkar Shirin BBNaija Ne, MURIC Ta Goyi Bayan Hisbah

  • Kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC ta goyi bayan matakin da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta dauka na gayyatar iyayen wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau a 2021, Shatu Garko
  • Dama tun bayan nasarar ta kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, Haruna Ibn-Sina ya bayyana cewa gasar ta ci karo da koyarwar addinin musulunci don haka ba za su lumunta ba
  • Sai dai a ranar Laraba, bayan tattaunawar darektan MURIC, Ishaq Akintola da manema labarai, ya ce duk da rufe jikinta da tayi, haramun ne mace ta yi rangwada gaba dubbannin maza

Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC, ta goyi bayan hukumar Hisbah akan gayyatar iyayen Shatu Garko, wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Najeriya a shekarar 2021, akan shigarta gasar, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rudani: Hisbah ta ce babu batun gayyatar iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko, ta yi bayani

Garko, wacce ‘yar asalin jihar Kano ce ta zama mace ta farko mai hijabin da ta lashe gasar tun bayan farawa a shekarar 1957.

Shatu Garko: Gasar Sarauniyar Kyau Tamkar Shirin BBNaija Ne, MURIC Ta Goyi Bayan Hisbah
Gasar Sarauniyar kyau kamar BBNaija ne, MURIC ta mara wa Hisbah baya. Photo credits: Facebook/Isah Waziri Arg, Instagram/shatu.garko
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai Haruna Ibn-Sina, kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano, ya yi alawadai akan shigar Garko gasar inda ya ce hakan ya saba wa koyarwar addinin musulunci.

Hukumar ta kudirci gayyatar iyayen Garko don su amsa tambayoyi

Ya kara da cewa za su gayyaci iyayen sarauniyar kyau din don su amsa tambayoyi gaban hukumar.

Yayin tattaunawa da The Punch a ranar Laraba, Ishaq Akintola, darektan MURIC ya ce zunubi ne shigar Garko gasar duk da ta sanya hijabi musamman “yin rausaya gaban dubbanin jama’a su na kallonta da idanunsu.”

Akintola ya kara da cewa shiga gasar sarauniyar kyau kamar shiga shirin BBNaija ne.

Kara karanta wannan

Kotu ta bukaci Shehi a Dubai ya biya tsohuwar matarsa $734m da 'ya'yansu

Ya ce yanzu babu tarbiyya a gidaje

Kamar yadda yace:

“Da kyau, meyasa ku ke ganin Najeriya a cikin tashin hankali da matsaloli? Saboda yanzu babu tarbiyya a gidaje. Ya aka yi iyayenta su ka bar ta taje gasar? Duk da shekarunta 18 amma ai karkashin iyayenta take a musulunci.
“Ya kamata mata su yi shigar mutunci su kuma lullube jikinsu daga idanun jama’a. Shigar ta gasar duk da hijabin jikinta ai ta yi rangwada gaban dubbannin maza wadanda su ka dinga kallonta da idanunsu. Hakan bai dace ba.
“Yayin gasar, mata su na rausaya a bainar jama’a inda su ke sa dan kamfai da rigar mama da sauransu. Bai dace musulma ta shiga irin wannan gasar ba saboda musulunci addini ne na mutane masu da’a da kunya, masu daraja da kima wadanda ba sa nuna tsiraicinsu ga dubbannin jama’a.”

Ya nuna rashin jin dadinsa akan shigarta gasar

A cewarsa ba su ji dadin yadda musulma ta shiga irin wannan gasar wacce ta ke rangwada gaban mutane iri-iri ba.

Kara karanta wannan

Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko

Ya kara da cewa kamar shiga BBNaija ne sanye da hijabi ko kuma yin shiga irin ta musulunci amma mace ra shiga shirin BBNaija wanda ake haska mace don miliyoyin ‘yan Najeriya su dinga kallonta.

Dama tun a baya Akintola ya hori iyaye akan su daina barin yaransu su na shiga shirye-shirye irin na BBNaija.

Asali: Legit.ng

Online view pixel