Yanzu-Yanzu: Buhari ya dira Maiduguri mintuna bayan harin da Boko Haram ta kai filin jirgi

Yanzu-Yanzu: Buhari ya dira Maiduguri mintuna bayan harin da Boko Haram ta kai filin jirgi

  • Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno jim kadan bayan harbe roka da Boko Haram ta yi a birnin
  • Shugaba Buhari ya kai ziyarar ne domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Jihar Borno ta yi kuma ana sa ran zai koma Abuja a yau Alhamis
  • Gwamna Babagana Zulum da shugababannin hukumomin tsaro na kasa ne suka tarbi Buhari a filin jirgi sannan aka saka shi a mota suka shiga birnin Maiduguri

Borno - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin ziyarar aiki ta kwana daya mintuna kadan bayan 'yan Boko Haram sun harba roka cikin filin jirgin sama na Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Manyan ma'aikatan gwamnati sun yi wa Buhari rakiya zuwa Borno, jirginsa ya dira a Maiduguri misalin karfe 11.45 na safiyar yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Kasa Buhari ya kama hanyar zuwa Maiduguri, jihar Borno

Yanzu-Yanzu: Buhari ya dira Maiduguri mintuna bayan harin da Boko Haram ta kai filin jirgi
Buhari ya isa Maiduguri bayan Boko Haram sun harba roka. Hoto: The Nation

Gwamna Zulum ya tarbi Buhari

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya na filin jirgin tare da dukkan shugabannin tsaro, da suka isa jihar domin tarbar Buhari.

Wannan ziyarar ita ce ta biyu da Buhari ke kai wa Borno cikin watanni 6 da suka gabata tun ziyarar da ya kai karshe a ranar 21 ga watan Yunin 2021 inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin ta yi da NEDC.

Nan take aka dauki Shugaban kasar a mota daga filin jirgin zuwa babban makarantar Shiekh Tijanni Bolori da ke bayan Quarter Maiduguri.

Zulum ya yi kira ga al'ummar jiharsa su fito kwansu da kwarkwata su tarbi Shugaba Buhari a kokarin da ake yi na mayar da su gidajensu da kuma ayyukan alheri da shugaban kasar ya yi musu a shekaru shida da suka gabata.

Kara karanta wannan

Ku fito kwai da kwarkwata ku tarbi Buhari hannu bibbiyu, Zulum ga 'yan jihar Borno

An gano cewa an bada umurnin rufe wasu hanyoyi da kasuwanni da ke cikin birnin yayin ziyarar shugaban kasar har sai ya tafi misalin karfe 2 na rana.

Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin Maiduguri

Tunda farko, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun harba makamai masu linzami a filin jirgin sama da ke yankin Ngomari a Maiduguri yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shirin sauka a birnin yau Alhamis.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, daya da cikin makaman masu linzami ya tsallake har zuwa Ajilari, kusa da filin jiragen sama na Maiduguri inda sansanin sojoji ya ke.

Majiyoyi sun ce mutum daya ya rasa ransa a Ngomari yayin da wasu suka samu raunika a yankin Ajilari.

Alamu suna nuna cewa, maharan sun daidaita tare da saitar filin saukar jiragen saman ne saboda makaman sun sauka 10:45 na safe, mintoci kadan kafin isar Buhari birnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel