Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara

Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara

- Mummunan gobarar ta kone shaguna a kalla 63 a kasuwar Tudun Wada da ke Gusau

- Gwamnan jihar, Bello Matawalle ya ziyarci kasuwar inda ya jajantawa musu kan afkuwa ifti'la'in

- Gwamnan ya kuma yi alkawarin sake gina shaguna da suka kone tare da bawa yan kasuwar tallafi

Gobara a ranar Lahadi ta kone a kalla shaguna 63 a kasuwar Tundun Wada da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An kyautata zaton wutan ta taso ne daga wani shagon siyar da kifi wutar shagon ke da tangarda.

Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara
Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja

Yayin ziyarar da ya kai wurin da abin ya faru, Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya jajantawa wadanda abin ya shafa ya ce su dauki abin a matsayin kaddara ne daga Allah.

Ya shawarci yan kasuwan su rika duba kayayyakin wutan lankarkinsu kafin su rufe shagunansu idan sun kammala ciniki na kowanne rana.

Ya ce gwamnatin jihar za ta sake gina shagunan 63 da wutan ya shafa kuma ya umurci kantoman riko na karamar hukumar Gusau ya fara aiki nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC Ta Kusa Rushewa, In Ji Gwamna Aminu Tambuwal

Gwamna Matawalle ya kafa kwamiti karkashin jagorancin malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Umar Kanoma domin bincika irin asarar da yan kasuwan suka yi ya bada rahoto cikin kwanaki bakawai domin gwamnatin jihar ta san irin tallafin da za ta yi wa yan kasuwan.

Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da taimakawa yan kasuwa da sauran masu treda domin habbaka tattalin arzikin jihar.

A wani rahoton, kun ji Rundunar yan sandan jihar Sokoto, a ranar Alhamis, ta ce ta kama a kalla mutane 17 kan zargin fashi da makami, garkuwa da mutane da wasu laifuka a jihar.

Mr Kamaldeen Okunlola, kwamishinan yan sandan jihar ne ya sanarwar manema labarai hakan a Sokoto, Vanguard ta ruwaito.

Okunlola ya ce rundunar a ranar 4 ga watan Maris ta kama wani Jabbi Wanto kan hadin baki da sace mutane biyu a Tamba Garka a karamar hukumar Wurno na jihar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164