Ba za ta saɓu ba: Za mu hukunta doddani da ke cin zalin jama'ar mu, Gwamnatin Abia

Ba za ta saɓu ba: Za mu hukunta doddani da ke cin zalin jama'ar mu, Gwamnatin Abia

  • Gwamnatin jihar Abia ta umarci kama dodanni tare da gurfanar da su matsawar wani dodo ya razanar ko ya ci zarafin baki ko mazauna gari yayin bikin kirsimeti
  • Sakataren gwamnatin jihar, Chris Ezem ya saki takarda wacce ta bayar da umarnin kama duk wani dodon da aka kama ya na toshe tituna da dakatar da ababen hawa
  • Gwamnati ta dauki matakin ne don tabbatar da ta samar da cikakken tsaro ga jama’an garin da dukiyoyinsu yayin shagulgulan kirsimeti da sabuwar shekara mai karatowa

Abia - Gwamnatin jihar Abia ta umarci kama duk wani dodo tare da gurfanar da shi matsawar aka kama shi da cutar da mazauna da baki a jihar yayin shagalin kirsimeti da sabuwar shekara, The Nation ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin jihar, Chris Ezem, a wata takarda ya ja kunnen dodanni akan dakatar da titina da ababen hawa, inda yace matsawar aka kama zai fuskanci fushin shari’a.

Gwamnatin jihar Abia ta ce ta dauki matakin ne don tabbatar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma yayin shagulgulan da ke karatowa.

Gwamnatin Abia za ta hukunta 'doddani' saboda cin zalin mazauna jihar ta
Za mu hukunta doddani da ke cin zalin jama'ar mu, Gwamnati Abia
Asali: Facebook

Gwamnatin ta shawarci mazauna da kai kara wurin jami’an tsaro

Gwamnatin jihar ta yi kira ga mazauna yankin akan kai karar duk wanda su ka samu yana aiwatar da hakan ga jami’an tsaro.

Kamar yadda takardar tazo:

“An janyo hankalin gwamnatin jihar akan yadda dodanni su ke toshe babbar hanyar Umuahia, babban birnin jihar Abia.
“Don haka gwamnatin ke bayar da umarnin dakatar da dodannin daga tsayawa kan hanya don amsar kudade daga masu ababen hawa da sunan shagalin kirsimeti, matsawar aka kama mai aikata hakan, zai fuskanci fushin shari’a.
“Jami’an tsaro za su dauki mummunan matakai akan yadda dodanni su ke cin karensu babu babbaka a titinan Umuahia.”

Gwamnatin ta ce zata tabbatar da tsaro a jihar yayin shagulgulan

Gwamnatin jihar ta ce tana farincikin tabbatar wa mazauna Abia da masu zuwa don bukukuwan cewa lafiyarsu da dukiyarsu a tsare su ke cikin lokacin shagulgulan nan.

Gwamnatin ta kara da shawartar duk wani dan Abia da kai rahoto akan duk wani abu da ya ga alamar zai iya kawo cikas ga tsaro a jihar.

Daga karshe The Nation ta bayyana yadda gwamnatin ta ke taya ‘yan jihar Abia murnan kirsimeti da fatan ganin sabuwar shekara lafiya.

Ya matsa a bashi kasonsa: Matashi ya maka mahaifiyarsa a kotu kan gadon mahaifinsa, mutane sun magantu

A wani labarin, wani matashi ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ya wallafa wani abu da abokinsa ya aikata.

A wata wallafa da OnyedikaAnambra ya yi a kafar sada zumunta ta zamani ya bayyana yadda mahaifin shakikin abokinsa ya rasu ya bar wa iyalansa dukiya.

https://hausa.legit.ng/news/1448883-ya-matsa-a-bashi-kasonsa-matashi-ya-maka-mahaifiyarsa-a-kotu-kan-gadon-mahaifinsa-mutane-sun-magantu/

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel