Zamfara: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a maboyarsu, sun samo shanu da miyagun makamai

Zamfara: 'Yan sanda sun ragargaji 'yan bindiga a maboyarsu, sun samo shanu da miyagun makamai

  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara ya sanar da cewa jami'ansa sun kai farmaki har maboyar 'yan bindiga inda suka halaka wasu miyagun
  • 'Yan sandan sun samu nasarar bankado wani farmaki da 'yan bindigan suka kai inda suka sace mutum 3, ciki har da jinjiri mai wata uku a duniya
  • Elkanah ya sanar da cewa, jami'an sun samo bindigogin takwas, shanun sata sittin da tara, bindigar harbo jiragen sama da sauransu

Zamfara - Jami'an 'yan sandan jihar Zamfara sun samo bindigogi takwas bayan kai samame wata maboyar 'yan bindiga da ke kusa da Bayan Ruwa a karamar hukumar Maradun ta jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce jami'ai na musamman ne suka kai samamen bayan samun bayanan sirri, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ceto wasu mutane da aka sace, sun yi ram da masu satar shanu

Zamfara: 'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga, sun samo bindigogi 8, shanun 69
Zamfara: 'Yan sanda sun kai samame maboyar 'yan bindiga, sun samo bindigogi 8, shanun 69. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Jami'an sun yi arangama da 'yan daban inda suka kashe da yawa daga cikinsu yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika.
“A yayin binciken wurin, an samo bindigogi takwas kirar AK47, bindigar harbo jirgin sama da alburusai masu tarin yawa," ya kara da cewa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Elkanah ya kara da cewa, rundunar ta bankado wani farmaki da 'yan bindiga suka kai kauyen Rughar Tudu tare da sace wasu mutum 3. Ya ce mutane ukun da suka sace sun hada da jinjiri mai wata uku.

Daily Trust ta ruwaito cewa, jam'ian 'yan sandan sun samo shanu sittin da tara bayan musayar wuta da suka yi da miyagun a kauyen Tudun Masu da ke karamar hukumar Bungudu. An mika sittin daga ciki zuwa hannu masu shi.

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

Kara karanta wannan

Da duminsa: Boko Haram sun kai sabon farmaki Borno, sun kone gidajen jama'a

A wani labari na daban, fusatattun jama'ar jihar Katsina sun mamaye babban titin Funtua zuwa Sheme na jihar Katsina tare da hana ababen hawa wucewa a titin Funtua zuwa Gusau kan farmakin da 'yan bindiga ke kai musu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wani matafiyi mai suna Imam Abubakar, ya sanar da cewa matafiya suna nan dankare a wurin sun kasa yin gaba ko baya.

"Ga mu nan a wurin, ba zan iya fadin yawan ababen hawa da ke titin nan ba da masu zanga-zanga suka tare. A yanzu da muke magana, muna jin harbin bindigar 'yan sanda dasojoji wadanda aka turo yankin, amma masu zanga-zangar sun rufe titin suna kona tayoyi," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel