Kaduna: Sarkin Zazzau Ya Bukaci Limamai Da Fastoci Su Fara Addu’o’i Na Musaman Kan 'Yan Bindiga

Kaduna: Sarkin Zazzau Ya Bukaci Limamai Da Fastoci Su Fara Addu’o’i Na Musaman Kan 'Yan Bindiga

  • Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli, ya umurci limamai da fastoci a masarautarsa su fara addu'a na musamman kan yan bindiga
  • Ambasada Nuhu Bamalli ya bayyana hakan ne cikin wata takarda da mai magana da yawun masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar
  • Sarkin ya kuma takaita ziyara zuwa fadarsa tare da mika sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasu da jajantawa wadanda suka yi rauni sakamakon harin yan bindiga

Kaduna - Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi kira ga dukkan limamai da fastoci da ke masarautar Zazzau su fara addu'a na musamman don ganin an samu zaman lafiya a yankin da ma kasa baki daya, Daily Trust ta ruwaito.

Bamalli, wanda ya bayyana hakan cikin takardar da mai magana da yawun masarautar, Malam Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar ya ce hakan ya zama dole ne saboda yawai kashe-kashe da hari da garkuwa da mutane da ake yi a masarautar.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

Kaduna: Sarkin Zazzau Ya Bukaci Limamai Da Fastoci Su Fara Addu’o’i Na Musaman Kan 'Yan Bindiga
Sarkin Zazzau Ya Umurci Fastoci Da Limamai Su Fara Addu’o’i Na Musaman Kan 'Yan Bindiga. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bukaci dukkan musulmi su fara yin addu'o'in na musamman a salloli biyar na kowanne rana yayin da kiristoci kuma a yayin addu'o'in su na coci don neman Allah ya kawo sauki, rahoton Daily Trust.

Basaraken, yayin da ya ke mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa 'yan uwansu ya kuma jajantawa wadanda suka samu raunuka sakamakon harin na 'yan bindiga daban-daban.

Sarkin ya kuma takaita yawan ziyarar da za a rika kai wa fadarsa.

Jihar Kaduna ta kasance tana fama da hare-haren yan bindiga na tsawon lokaci, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da yan bindiga ba sai dai kisa kawai.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawarsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a kan harin da aka kai a baya-bayan nan inda aka kashe mutum a kalla 40 a jihar.

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

Gwamnan, wanda Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya yi wa rakiya zuwa fadar shugaban kasar ya ce an san inda yan bindigan suke amma sojoji na duba adadin farar hula da abin zai shafa ne idan aka ce za a kai musu hari.

'Yan Bindiga Sun Kai Wa Matafiya Hari, Sun Sace Da Dama a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace matafiya da dama a kan hanyar Kaduna - Birnin Gwari a ranar Laraba bayan kai musu hari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A halin yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan harin da aka kai misalin karfe 11 amma an gano cewa mafi yawancin wadanda abin ya faru da su yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Wani shugaban al'umma, Muhammadu Umaru, ya shaida wa Daily Trust cewa hudu daga cikin makwabtansa suna daga cikin wadanda aka sace, ya kara da cewa yan sanda sun yi wa motoccin da suka kai 20 rakiya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Asali: Legit.ng

Online view pixel