Yanzu-Yanzu: Gwamnati ta sanar da ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Yanzu-Yanzu: Gwamnati ta sanar da ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

  • Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranakun da ma'aikatan gwamnati za su huta saboda hutun Kirsimeti da sabuwar Shekara
  • Ministan harkokin cikin gida ne ya bayyana wasu ranaku da yace gwamnati ta amince a yi hutun hade da zagayowar ranar dambe ta duniya
  • Hakazalika, ministan ya yi kira ga kiristocin Najeriya da su yi amfani da wannan lokacin don yiwa kasa addu'o'in alheri

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta sanar da ranakun 27 da 28 na watan Disambar 2021 da kuma ranar 3 ga watan Janairun 2022 a matsayin ranakun hutun Kirsimeti hade da ranar dambe ta duniya da na sabuwar shekara.

Wannan na fitowa ne daga sanarwar da ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya fitar a yau Laraba.

Ministan harkokin cikin gida
Yanzu-Yanzu: Gwamnati ta sanar da ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara | Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

A cikin sanarwar da ta iso Legit.ng Hausa da safiyar yau Laraba 22 ga watan Disamba, ministan ya taya kiristocin Najeriya da ke ciki da wajen kasa murnar Kirsimeti da zagayowar sabuwar shekarar.

Kara karanta wannan

Bincike ya bayyana asarar biliyoyi da gwamnati ta yi saboda dakatar da Twitter

A kalamansa, cewa ministan ya yi:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dole ne mu yi koyi da rayuwar Yesu Almasihu a cikin ayyukansa da koyarwarsa akan Tawali'u, Hidima, Tausayi, Hakuri, Salama da Adalci, wanda haihuwarsa ke nunawa. Wannan ita ce hanya mafi kyau ta kwatanta Almasihu da kuma bikin haihuwarsa."

Da yake bayyana kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman na rashin tsaro, ya roki kiristoci da sauran 'yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokacin domin yiwa kasa addu'o'in alheri.

Korona gaskiya ne, inji ministan

Aregbesola ya yi kakkausar suka ga ‘yan Najeriya da kada a sanya su cikin rudani game da cutar Korona, ya kuma lura da cewa cutar na kara daukar wani salo mai matukar hadari da cutarwa tare da bullar wani nau’i mai suna Omicron.

Ya kara da cewa:

"Wannan yana kira da a yi taka-tsan-tsan da alhakin da kuma ladabtar da kowa."

Kara karanta wannan

Hotunan ziyarar ta'aziyyar da Ganduje ya kaiwa Kwankwaso bisa rasuwar kaninsa

A karshe, Aregbesola ya gargadi dukkan ‘yan kasar da su ci gaba da mai da hankali tare da bayyana kwarin gwiwa cewa shekarar 2022 za ta kasance mafi alheri ga kowa.

Yana yiwa daukacin kiristoci barka da Kirsimeti da daukacin ‘yan Najeriya fatan shiga sabuwar shekara lafiya.

Kalli sanarwar.

Bidiyon 'yan sanda na raba wa masu mota kudi maimakon karba daga hannunsu

A kasar Amurka kuwa, jami'ai daga Sashen 'yan sanda na Ocala da ke Florida a Amurka, an gansu a cikin wani faifan bidiyo da ke rera taken Santa Claus.

A wani faifan bidiyo da Ayo Ojeniyi ya yada, wani jami’in dan sanda ya tare wata mata mai mota inda ya ce zai ba ta kudi $100 (N41,016). Da matar ta ji haka, sai ta tambaye shi ko da gaske ne zai yi hakan?

Bayan ya ba ta kudin, matar da ta kasa gaskata abin da ya faru a baya ta zabga kururuwa:

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan Majalisar Wakilai sun amince da Kasafin Kudin 2022, sun kara N700bn

"Na gode, Yesu!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel