Wani mai jinyar karaya ya yi karfin-hali, ya sace motar daukar marasa lafiya a jihar Kano

Wani mai jinyar karaya ya yi karfin-hali, ya sace motar daukar marasa lafiya a jihar Kano

  • Wani mai jinyar daurin karaya a kafa ya sace motar asibiti a wani kauye a garin Dawakin Tofa, Kano
  • Jami’an ‘yan sanda sun gano wannan motar daukar marasa lafiya da aka dauke a Babura, jihar Jigawa
  • Bincike ya nuna cewa mutumin da ya aikata wannan danyen aiki dan asalin garin Daura ne, jihar Katsina

Kano - An samu labarin wani mai jinya da ya sace motar asibiti. Abin ban mamakin shi ne wannan maras lafiya ya na fama da daurin karaya a kafa.

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa wannan abin ban mamaki da takaici ya faru ne a garin Kano.

‘Yan Sanda sun yi nasarar damke wannan barawo da ya sace motar daukar marasa lafiya a kauyen Takwasa, karamar hukumar Babura, jihar Jigawa.

Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun ce an gano wannan mota da aka dauke a jihar Kano a can kauyen Takwasa, a hannun wannan mutum da ya karye.

Ana zargin wannan mutumi da sungume motar daukar marasa lafiya da gawa, tattare da duk wasu magungunan da ake ajiyewa a cikinta saboda larura.

PoliceNG
Dakarun 'Yan sanda @PoliceNG
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jawabin kakakin 'yan sanda

Mai magana da yawun bakin Jami’an ‘yan sanda na reshen Jigawa, ASP Lawan Shi’isu, ya shaidawa manema labarai wannan a ranar Talatar nan.

“’Yan sanda sun gano motar a kauyen Takwasa, a Karamar Hukumar Babura, Jihar Jigawa, a hannun wani mutum ‘dan asalin Karamar Hukumar Daura ta Jihar Katsina, mai muguwar karaya a kafarsa.”
“An yi sanadiyyar gano motar ne bayan samun rahoton sace motar daukar marasa lafiyan kirar ‘Hummer Bus’ mara lamba a jikinta - da magungunan cikinta, mallakin Karamar Hukumar Ungogo, Kano.”
- ASP Lawan Shi’isu

Yadda aka gano barawon motar - NPF

A cewar ASP Lawan Shi’isu, an dauke wannan mota ne a wani kauye da ake kira Kanya Hora a Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano, kwanaki.

Bayan samun rahoton satar, sai ‘yan sandan da ke garin Babura su ka fara bincike domin gano inda motar ta shiga, ba a je ko ina ba kuwa sai aka gano ta.

An gano motar ne a ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, 2021. Yanzu haka ana cigaba da gudanar da bincike domin a iya kai wannan mutumi zuwa kotu.

'Danuwan Rabiu Musa Kwankwaso ya rasu

A makon nan aka ji cewa Inuwa Musa Kwankwaso ya rasu. Inuwa Musa ya yi fama da rashin lafiya kafin Allah ya dauki rayuwarsa a asibitin Aminu Kano.

Kamar dai yadda Musulmai suka saba, tuni an birne Marigayin a kauyensu na Kwankwaso a Garin Madobi, a jihar Kano inda dinbin mutane suka halarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng