Sanatan APC ya rabawa 'yan mazabarsa motoci 50, babura 500 da kayan gona a tashi daya

Sanatan APC ya rabawa 'yan mazabarsa motoci 50, babura 500 da kayan gona a tashi daya

  • Sanata Sa’idu Alkali ya yi rabon motoci, babura, kekunan dinki da kayan noma a Arewacin jihar Gombe
  • ‘Dan majalisar mai wakiltar Gombe ta Arewa ya raba wadannan kaya ne a karshen makon da ya wuce
  • Baya ga wadannan kaya na miliyoyi, Sa’idu Alkali ya samar da ruwan sha da tituna ga mutanensa

Gombe - Hukumar dillacin labarai na kasa ta rahoto cewa Sanata Sa’idu Alkali mai wakiltar Gombe ta Arewa, ya rabawa talakawansa kayan miliyoyi.

A ranar Lahadi, 19 ga watan Disamba, 2021, NAN ta fitar da rahoto cewa Sa’idu Alkali ya rabawa mutanen mazabarsa motoci, kayan gona da makamantansu.

Daga cikin abubuwan da ‘dan majalisar dattawan ya kyautar akwai motoci 50, babura 500, kekunan dinki 600, firji da kuma kayan feshi na noman rani.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Har ila yau, jaridar NNN tace Sa’idu Alkali ya yi rabon na’urori 1, 000 na casa da gyran shinkafa da wasu kayan aikin gona ga manoman da ke Arewacin Gombe.

Abin da ya sa na yi wannan alheri - Alkali

Da yake jawabi a wajen rabon kayan, Sanatan yace ya yi wannan kokari ne domin ya godewa mutanensa da suka sake zaben shi a karo na uku zuwa majalisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanatan APC
Saidu Alkali ya raba motoci
Asali: UGC

Sanata Alkali yace a shekarar nan ya gina ajujuwa a makarantu, dakunan shan magani, sannan ya samar da ruwan sha a wasu kauyukan da suke karkashinsa.

Baya ga haka, Alkali ya gina tituna a kananan hukumomi biyar da yake wakilta a majalisar dattawa; Dukku, Gombe, Kwami, Funakaye da kuma garin Nafada.

Wadannan duk su na cikin ayyukan mazabun da Sanatan ya kawowa yankin Gombe ta Arewa.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya ɗauki mataki kan mawaƙin da ya gwangwaje shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, da waƙar yabo

Gwamna da shugaban majalisa sun yaba

Mai girma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya halarci bikin rabon kayan, inda ya yabawa irin wannan sha-tara na arziki da Sanatan ya yi wa mutanensa.

Daily Nigerian tace baya ga Alhaji Inuwa Yahaya, shugaban majalisar dattawa na kasa, Ahmad Lawan ya samu halartar rabon kayan, ya yabawa abokin aikin na sa.

Kwastam ta samu N2.3tr a 2021

Dazu aka ji cewa kudin da Kanal Hameed Ali, Kwastam suka tara a asusun tarayyar Najeriya a shekarar 2021 ya kai N2.3tr inji wani babban jami’in hukumar ta kasa.

Timi Bomodi yace abin da aka yi tunanin samu a bana shi ne N1.68tr, amma daga Junairun bana zuwa Disamba, kudin-shigan da ya fito daga kwastam ya kai N2.3tr.

Asali: Legit.ng

Online view pixel