Wata mummunar gobara ta kone shaguna sama da 300 ƙurmus a jihar Sokoto

Wata mummunar gobara ta kone shaguna sama da 300 ƙurmus a jihar Sokoto

  • Wata gobara da ta ɓarke a kasuwar Kara dake cikin kwaryar birnin Sokoto ta yi wa yan kasuwa mummunan ɓarna
  • Gwamna Tambuwal na jihar Sokoto ya jajantawa yan kasuwan tare da rokon su rungumi kaddara da imaninsu, domin komai daga Allah ne
  • Rahoto ya nuna cewa gobarar, wacce ta barke tun da subahi ta lakume shaguna sama da 300

Sokoto - Sama da shaguna 300 sun ƙone ƙurmus yayin da wata gobara ta tashi a kasuwar Kara, dake kwaryar birnin Sokoto, kamar yadda dailytrust ta rahoto.

Har yanzun ba'a gano musabbabin godabarar ba, amma a cewar wani shaidan gani da ido wutar ta fara ne da misalin karfe 4:00 na subahi.

Mun samu rahoto mabanbanta kan daga inda wutar ta tashi, wani yace wutar ta tashi ne daga sashin masu siyar da hatsi kafin da bazu zuwa sauran sassan kasuwar.

Jihar Sokoto
Wata mummunar gobara ta kone shaguna sama da 300 ƙurmus a jihar Sokoto Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mutane sun tafka asara

Ɗaya daga cikin yan kasuwan da abun ya shafa, Jamilu Isa, yace gaba ɗaya dukiyarsa ta dulmiye a wannan gobarar.

"Na rasa komai dake shago na gaba ɗaya, haka ma makota na suka tafka wannan asara," inji shi.

Kakakin yan kasuwan, Tukur Balarabe, yace sama da shaguna 300 sun kone ƙurmus kafin a shawo kan gobarar.

Shugaban ƙungiyar yan kasuwan jihar Sokoto, Alhaji Chika Sarkin Gishiri, yace wutar da lalata dukiyoyi da suka kai darajar miliyoyin nairori.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar Sokoto ta dubi Allah ta kawo wa yan kasuwan ɗauki, ta hanyar samar da musu da tallafin kudi.

Tambuwal ya jajantawa yan kasuwan da abun ya shafa

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, wanda yana ɗaya daga cikin mutanen da aka sanar da su, ya jajantawa mutane tare da rokon su rungumi kaddara.

"Mun san cewa duk abin da ya faru da musulmi mai kyau ko mara kyau duk daga Allah ne. Dan haka ina son ku dauka haka Allah ya so, kuma ku nemi zabin sa."

Gwamnan, wanda mataimakinsa, Manir Dan’iya, ya wakilta, ya umarci kwamishinan kasuwanci da shugaban yan kasuwa reshen Sokoto, su ɗauki alƙaluman barnar da wutar ta yi.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya yi bayani dalla-dalla kan zuwansa Legas da rashin zuwa jaje Sokoto

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kare kansa daga sukar da yake sha bayan zuwa Legas a lokacin da aka kashe mutane a Sokoto .

Malam Garba Shehu, yace ba kaddamar da littafi ya kai Buhari Legas ba, ainihin makasudin zuwansa dan jiragen ruwan sojoji ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel