Gwamnatin Neja ta kama almajirai 104 masu kananan shekaru da aka shigo dasu

Gwamnatin Neja ta kama almajirai 104 masu kananan shekaru da aka shigo dasu

  • Gwamnatin jihar Neja ta kame almajirai 104 tare da mayar dasu inda suka fito daga jihar Sokoto, inji rahotanni
  • Gwamnatin jihar ta Neja ta bayyana cewa, har yanzu bata dage dokar haramta almajiranci da barace-barace a jihar ba
  • Hakazalika, gwamnati ta koka kan yadda ake daukar yara masu kananan shekaru daga nisan duniya zuwa wani yankin

Jihar Neja - Jaridar Punch ta rahoto cewa, gwamnatin jihar Neja ta mayar da almajirai 104 da aka kama a kofar Minna zuwa jihar Sokoto.

Darakta Janar na hukumar kare hakkin yara, Maryam Kolo, wacce ta bayyana hakan a ranar Litinin a Minna, ta ce almajiran na tsakanin shekaru hudu zuwa 10, kuma sun yi tattaki ne daga Sokoto zuwa Minna a cikin mota.

Ta bayyana hanyoyin jigilar almajirai daga nesa kuma a wannan lokaci na hunturu a matsayin tsagwaron mugunta.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Gwamnan jihar Neja
Gwamnatin Neja ta kama masu shigo da almajirai masu kananan shekaru daga nisan duniya | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Kolo ta bayyana damuwarta cewa duk da matakan da gwamnati ta dauka na hana afkuwar irin wannan lamari, har yanzu wasu mutane na samun hanyoyin shigo da yara cikin jihar da sunan neman ilimi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarta:

"Muna ba da himma sosai. Mun yi matukar mamakin yadda wani zai shigo cikin jihar da yara 104 tun daga Jihar Sokoto zuwa Jihar Neja da sunan makarantar Islamiyya ba tare da an ba su abinci ko kudi ba."

Kolo ta kara tabbatar da cewa matakin da gwamnatin jihar ta dauka na hana almajiranci da barace barace a kan tituna har yanzu yana nan daram.

Ta kara da cewa rashin tausayi ne a tura yaro dan shekara hudu ya yi tafiya mai nisa da sunan almajiranci.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, wani mutumin da aka samu yaran a hannunsa ya ce ya dauko yaran ne daga garin Illela da ke Jihar Sokoto, ya ce yana kawo yaran Jihar Neja ne domin almajiranci.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

Ya ce akwai tsangayar almajirai a Angwan Biri da ke cikin karamar hukumar Bosso, inda yaran za su zauna su yi karatu.

Tun a shekarar 2020 ne gwamnatin jihar Neja ta haramta dukkan nau'ikan barace-barace a fadin jihar ciki har da almajiranci, kamar yadda The Guardian ta rahoto.

Sai dai, rahotanni da dama sun bayyana har yanzu akan samu almajirai a wasu yankunan jihar duk da kasancewar dokar.

Gwamnatin Kaduna ta ce ta ceto yaran Almajirai 160 a Kaduna

A wani labarin daban, Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ta ceto yaran Almajirai guda 160 daga makarantu da gidajen da basu dace ba a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin yaran sun fito ne daga jihohi 13 a yankin arewa da kudancin kasar yayinda sauran suka fito daga Jumhuriyar Benin, Burkina Faso da kasar Nijar.

Tsarin karatun Almajiranci shine inda yara ke barin gidajensu zuwa nesa don neman ilimin addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gano masu daukar nauyin ta'addanci a jiharsa, ya saka ranar fallasa su

Asali: Legit.ng

Online view pixel