Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Labari da duminsa: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

  • Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana yadda wani kamfanin kera kayayyakin katako na Alibert ya kone kurmus
  • A yau ne da safe aka ce wata mummunar gobara ta kama a wannan kamfani, lamarin da ya haifar da tsoro
  • A cewar majiyoyi, lamarin ya kai ga raunatar wasu masu gadin kamfanin har mutum biyu kafin a kashe wutar

Kano - Gobara ta kone wani katafaren kamfanin kera ababen katako da ke Kano mai suna Alibert Furniture.

Daily Nigerian ta tattaro cewa gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar yau Litinin, inda ta kone kamfanin da ke kan hanyar Murtala Mohammed a cikin babban birnin kasar.

An tattaro cewa jami’an tsaro biyu na kamfanin sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti.

Gobara a jihar Kano
'Yanzu-Yanzu: Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano| Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Duk da cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, shaidu sun alakanta gobarar da matsalar wutar lantarki da ta samu daga taransifomar kamfanin.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki a gidaje a Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami’an kwana-kwana sun yi nasarar kashe gobarar amma har yanzu wasu sassa na ginin na ci gaba da cin wuta har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Wani ganau ya shaidawa Daily Trust cewa gobarar:

“Ta fara ne da safiyar yau yayin da muke nan muna kokarin samun abin da za mu ci. Nan da nan, sai muka ga mutane suna tururuwa don neman tsira.
"Dukkanmu mun fice don ba da taimako amma saboda girman lamarin, ba mu iya yin komai ba wajen shawo kan gobarar har sai da jami'an kashe gobara suka zo wadanda su ma suka yi kokari sosai kafin a kashe gobarar."

Bayan rugujewar gini, mummunar gobara ta kone gine-gine a Legas

A wani labarin, an samu hargitsi a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, yayin da wata gagarumar gobara ta cinye wasu gine-gine da shaguna a Owode Onirin, daura da unguwar Ikorodu Road a Legas.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Vanguard ta rahoto cewa a lokacin da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, suka isa wurin da lamarin ya faru, wasu fusatattun matasa sun far musu.

An ce matasan sun kai wa jami’an hari ne saboda rahotanni sun ce sun isa wurin a makare bayan an yi ta kiran su yayin da wutar ta kama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel