Amaryata ta yi barazanar kashe uwar gidana da yayana, Dan Allah ku raba mu, Miji ga Kotu

Amaryata ta yi barazanar kashe uwar gidana da yayana, Dan Allah ku raba mu, Miji ga Kotu

  • Wani magidanci ya garzaya kotu yana neman alkali ya raba aurensa da fitinanniyar matarsa dan ta fara barazanar kashe masa iyali
  • Magidancin yace amaryarsa ta fara barazanar kashe uwargida da yayansu guda hudu saboda tana son zama ita kaɗai
  • Matar ta zargi maigidan nata da cin amanarta, ta hanyar neman wasu mata yana kwanciya da su

Lagos - Wani magidanci ɗan shekara 59, Adeoye Akintoye, ya roki kotun kostumare a Igando, jigar Legas, ta raba aurensa da amaryarsa Modupe cikin gaggawa.

A rahoton The Nation, magidancin ya shaida wa kotun cewa matar ta yi barazanar hallaka matarsa ta farko da kuma ƴaƴan da suka haifa.

Kotu a Legas
Amaryata ta yi barazanar kashe uwar gidana da yayana, Dan Allah ku raba mu, Miji ga Kotu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Akintoye yace:

"Lokacin da muka haɗu na shaida mata ina da mata da ƴaƴa hudu, amma duk da haka ta samu ciki tare da ni."

Kara karanta wannan

Masu yi da gaske: Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ta mun barazanar zata kashe kanta idan na ƙi aurenta. Da farko ta nemi na saki matata ta farko dan ta zama ita kaɗai ke da ni amma da naƙi yarda, shi ne ta yi baranar kashe ta da yayanta."

Amaryata ta cika fitina - Akintoye

Magidancin ya kuma zargi matar ta sa ta biyu da rashin son zaman lafiya da neman fitina a kowane lokaci.

"Ta zo har coci na tare da ɗan da muka haifa ta bayyana kan ta a matsayin matata, na gargaɗe ta kada ta kuskura ta yi haka saboda bana son a san ina da mata biyu."
"Cocin mu ta na yaƙi da auren mace fiye da ɗaya. Yanzun sai an yi mun hukunci mai tsanani saboda Modupe ta tona mun asiri."

Shin ta amsa laifin ta?

Da take martani zargin, Modupe yar kimanin shekara 36, ta zargi mai gidanta da halin neman mata.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da bindigu

Vanguard ta rahoto Modupe tace:

"Na kama shi dumu-dumu a gado da wasu yan matan shi. Baya sauke nauyin dake kansa na biya mun bukatuna."

Alkalin kotun, mai sharia Adeniyi Koledoye, ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa 10 ga watan Fabrairun shekara mai kamawa.

A wani labarin na daban kuma Asirin wasu ma'aurata da suka siyar da jariri dan wata daya ya tonu

Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Ogun sun yi ram da wasu ma'aurata bisa zargin siyar da jaririn da suka haifa ɗan wata ɗaya.

Punch ta ruwaito cewa ma'auratan mata da miji, sun siyar da jaririn ne kan kuɗi naira dubu N50,000 ga wata mata da har yanzun ake nema ruwa a jallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel