Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta yin taron bukukuwa a harabar makarantu

Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta yin taron bukukuwa a harabar makarantu

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta hana yin duk wani taro na shakatawa, biki, shagulgula da sauransu a harabar makarantun gwamnatin da ke fadin jihar
  • Sakataren gwamnatin na ma’aikatar ilimi, Dr Yusuf Saleh ya bayar da wannan sanarwar a wata tattaunawa da manema labarai su ka yi dashi
  • Saleh ya ce gwamnatin ta dauki wannan matakin ne saboda dakatar da lalata kayan aikin makaranta tare da satar da jama’an su ke yi yayin shagulgulan

Jihar Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta hana yin duk wani taro, biki, sha’ani da sauran harkokin tara jama’a a harabar makarantun gwamnati da ke jihar, The Nation ta ruwaito.

Sakataren gwamnatin na ma’aikatar ilimi, Dr Yusuf Saleh ne ya sanar da hakan a wata tattaunawa da wakilin NAN ya yi da shi a Kaduna.

Kara karanta wannan

Da duminsa: An garkame makarantu a Niger kan shirin kai farmakin 'yan bindiga

Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta yin taron bukukuwa a harabar makarantu
Gwamnatin Kaduna ta hana yin taron bukukuwa a harabar makarantun jihar. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Saleh ya ce an dauki wannan matakin ne don bayar da kariya ga dukiya da kayan amfanin makarantu daga mabarnata.

Saleh ya ce su na kashe kudade wurin gyara shiyasa su ka dauki matakin

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Saleh ya ce:

“Tsawon lokaci ana amfani da makarantunmu wurin yin harkoki da shagulgula amma daga karshe sai ka ga an lalata kayan amfani.
“Kullum mu na samun korafi da bukatu daga jama’a akan gyara gine-gine ko kuma sauya wasu kayan amfanin makarantu, kuma muna amfani da makudan kudade wurin yin hakan ne.
“Don haka mun dauki matakin kare kayan amfanin makarantu ta wannan hanyar.”

Ya ce sun tura wasiku ga shugabannin makarantun

Ya bayyana yadda tuni su ka tura takardu ga shugabannin makarantun firamare da sakandare, inda aka umarcesu akan hana amfani da harabar makarantu wurin yin taro da bukukuwa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

A cewarsa akwai wasu makarantun da ba su da katanga, inda ya bayyana shirinsu na yin katangun da za su kewaye ko wacce makaranta da ke jihar.

Ya kara ca cewa ma’aikatar ilimin tare da hadin guiwar ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida har da hukumar kula ta jihar za su samar da isasshen tsaro a makarantun.

Gwamnati za ta samar da isasshen tsaro a makarantu

A cewarsa za su yi kokarin ganin sun samar da tsaro dangane da matsalolin da wasu makarantu su ke fuskanta.

Yayin tsokaci dangane da wannan ci gaban, Tijjani Aliyu, shugaban ma’aikatan KADBEAM ya yaba wa gwamnatin akan wannan matakin na kare kayan amfanin makarantun.

Ya ce hakan zai taimaka wurin rage asarorin da makarantu su ke tafkawa yayin taro ko kuma shagulgulan da ake yi a cikin harabobinsu.

Ya kara da bayyana yadda su ka tattauna a taron masu ruwa da tsakin KADBEAM akan matsalolin ilimin yara mata da ke jihar tare da rokon gwamnati akan samar da hanyoyin kariya ga kayan amfanin makarantu.

Kara karanta wannan

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Turji, da wakar yabo

Ya kara da bayyana yadda masu ruwa da tsakin su ka nuna goyon baya da bukatar neman hadin kan jama’an gari wurin kulawa da kayan amfanin makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel