Tsadar fetur, rikicin APC, yajin-aikin ASUU da abubuwa 3 da za a fuskanta a shekarar 2022

Tsadar fetur, rikicin APC, yajin-aikin ASUU da abubuwa 3 da za a fuskanta a shekarar 2022

  • Saura kusan makonni biyu ayi sallama da shekarar nan ta 2021, a shiga sabuwar shekara ta 2022
  • Akwai wasu manyan batutuwa da za su zama kanun labarai a badi, daga ciki akwai batun tsaro
  • Zaben 2023 da siyasar cikin gidan jam’iyyar APC su na cikin abubuwan da za su cika gari a badi

Nigeria - Nan da ‘yan kwanaki kadan ne za ayi ban kwana da shekarar 2021. Duniya ta fara hange da lissafin sabuwar shekara ta 2022 da za a shiga.

Vanguard ta tattaro jerin wasu muhimman abubuwa da za su cika wannan shekara ta 2022 mai zuwa.

Ana sa ran cewa daga cikin wadannan batutuwa da za su kanun-labarai a 2022, akwai maganar janye tallafin man fetur da shirin babban zaben 2023.

1. Zaben 2023

Shakka babu siyasar zaben 2023 da rikicin APC su na cikin labaran da za su cika gari a badi. Zaben shugabanni da neman tikitin jam'iyyar APC zai kara kamari.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Labarin Amare da Angwaye 10 da suka mutu daf da aurensu ko bayan biki

Ana sa ran za a gwabza tsakanin irinsu Bola Tinubu da wasu jiga-jigan APC. Akwai yiwuwar ‘yan siyasa su fara sauya-sheka a cikin wannan shekarar da za a shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Tallafin man fetur

A tsakiyar shekara mai zuwan ne gwamnatin tarayya ta ke shirin janye tallafin mai. Hakan zai sa litar fetur ya kai N340, wannan zai iya jawo zanga-zanga a Najeriya.

3. ASUU

Rahoton yace babu mamaki kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta sake komawa yajin aiki a 2022. Malaman na ikirarin gwamnatin tarayya ta saba alkawuran da ta yi.

Buhari
Buhari da hafsoshin tsaro a taro Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

4. COVID-19

Har yanzu Duniya ba ta gama yin sallama da annobar COVID-19 ba. A karshen 2021 aka samu bullar sabon nau’i na Omicron, wanda yanzu haka ya shigo kasar nan.

5. Nnamdi Kanu

Shari’ar Nnamdi Kanu da Sunday Igboho za su karade ko ina a shekara mai zuwa, musamman yadda gwamnatin Buhari ta nuna za ta iya yi wa jagoran IPOB afuwa.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano zai angwance da galleliyar budurwa, tsohuwar zumansa nan kusa

6. Rashin tsaro

Rashin tsaro na cikin wata matsalar da za a shiga sabuwar shekara da ita. ‘Yan bindiga su na cigaba da yin ta’adi har gobe musamman a garuruwan Arewa maso yamma.

Janye tallafin fetur

Gwamnoni su na goyon bayan a kara farashin fetur. Har an ji cewa Jihohi za su biya tsofaffin ma’aikata duk wasu fansho da suke bi bashi idan aka janye tallafin mai.

Kungiyar Gwamnoni ta bayyana wannan matsaya ne bayan wani taro da tayi a makon jiya. Idan gwamnatin tarayya ta janye tallafi, farashin litar mai zai iya kai N340.

Asali: Legit.ng

Online view pixel