Gwamnoni 36 sun goyi bayan Buhari a kan janye tallafin mai, a maida litar fetur N340

Gwamnoni 36 sun goyi bayan Buhari a kan janye tallafin mai, a maida litar fetur N340

  • Kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF tayi wani zama na musamman a tsakiyar makon nan
  • Shugaban NGF, Dr. Kayode Fayemi yace gwamnoni sun amince da batun janye tallafin man fetur
  • Domin a rage radadin cire tallafin, gwamnonin kasar za su biya tsofaffin ma’aikata bashin fansho

Abuja - Kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF tace jihohin kasar nan za su dauke nauyin duk wasu bashin fansho da ake binsu a cikin shekarar 2022 mai zuwa.

Jaridar nan ta The Cable tace gwamnonin sun bayyana haka ne a karshen wani zama na musamman da aka yi a ranar Laraba, 15 ga watan Disamba, 2021.

Kungiyar ta NGF tace za su biya tsofaffin ma’aikata fanshonsu ne idan an janye tallafin man fetur.

A takardar bayan taro da shugaban NGF, gwamnan Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya fitar, an ji cewa gwamnonin sun yarda su biya bashin fanshon da ake binsu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta karbo sabon bashi daga bankin muslunci saboda wasu dalilai

Kayode Fayemi yake cewa gwamnonin jihohin za su yi hakan ne domin a rage radadin da za a ji da farko idan gwamnatin tarayya ta janye tallafin man fetur.

Gwamnoni 36
Gwamnoni tare da Buhari Hoto: www.tvcnews.tv
Asali: UGC

Mu na tare da Muhammadu Buhari - NGF

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce za ta janye tallafin man fetur a shekara mai zuwa, sai a shigo da wani tsari na biyan talakawa N5, 000 duk wata.

Kayode Fayemi a matsayinsa na gwamnan gwamnoni yace sun amince da wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka na biyan tallafin zirga-zirga.

“A game da shirin kafa tsarin fansho na CPS na gwamnatoci, wannan zai sa jihohi su iya biyan bashin kudin fanshon da ake binsu.”
“An amince cewa biyan wadannan kudi ya na cikin nauyin da ke kan gwamnati domin su ragewa talaka radadin janye tallafin mai.” – NGF.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnonin Arewa ta Gabas sun shiga ganawar sirri a Yobe

Kwamishinonin kudi na jihohi 36 za su shigo da wannan tsari na CPS ta hanyar kawo dokar fansho da kafa hukuma ta musamman da za ta kula da lamarin.

Baya ga haka, gwamnatocin jihohi za su sa hannu a tsarin nan na biyan talakawa tubus N5, 000. Jaridar Tribune ta fitar da wannan rahoto a yammacin Alhamis.

Ma'aikata a Legas, su shar

Gwamnatin Legas ta bada sanarwar biyan ma’aikata tukwuicin goron zuwan shekarar 2022. Gwamna Babajide Sanwo Olu ya bayyana wannan a wata sanarwa.

Sanwo Olu ya ba ma'aikatan jihar Legas mamaki da wannan kyauta, ya yi alkawarin zai biya kowa 30% na albashinsa a tare da kudin aikin watan Disamban nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel