Abin tausayi: Labarin Amare da Angwaye 11 da su ka mutu daf da aurensu ko bayan biki

Abin tausayi: Labarin Amare da Angwaye 11 da su ka mutu daf da aurensu ko bayan biki

Duk da dai an san cewa kowane rai za ta mutu, kuma mutuwa na da matukar ciwo, amma babu mutuwa mai ratsa zuciya kamar ta saurayi ko budurwa

A ‘yan watannin bayan nan, an samu labarin wasu mace-mace a jihohin Najeriya da suka jijjiga har wadanda ba na-kusa da wadanda lamarin ya shafa ba

Dalili kuwa shi ne wadannan mutane sun rasu ne a daidai lokacin da ake shirin bikin aurensu, ko kuma jim kadan bayan sun yi aure ko ana tsakar biki

Legit.ng Hausa ta tattaro labaran irin wadannan mutuwa masu ban tausayi:

1. Fatima Hassan Fari

A farkon shekarar nan Fatima Hassan Fari ta rasu. Wannan Baiwar Allah ta cika ne yayin da ake saura awanni uku a daura mata aure a Funtua, jihar Katsina.

2. Hussaina Baffa Bello

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A babban birnin jihar Yobe watau Damaturu, sojoji sun taba yin sanadiyyar mutuwar wata Hussaina Baffa Bello, ana saura ‘yan kwanaki ta zama Amarya.

Motar sojoji ne ta ki bin dokar, ta latse wannan budurwa mai shekara 19 ta na cikin keke-napep.

3. Jamilu Abdulhamid

Dateline ta kawo labarin Jamilu Abdulhamid da sahibarsa Saratu Abdul Salisu da suka yi aure a Kano. A kan hanyarsu ta zuwa Abuja, suka yi hadarin mota.

Jamilu Abdulhamid ya yi shirin wucewa da Amaryarsa zuwa garin Edo, inda za su zauna, sai ya hadu da ajalinsa. Saratu ta yi ta jinya a asibiti bayan hadarin.

4. Samuel Yarling

A watan Maris aka ji labarin wani Samuel Yarling wanda ya rasu a ranar da za a daurea masa aure. Mutuwar Yarling ta gigita danginsa da na amaryarsa a Jos.

Kara karanta wannan

Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari

Amare da Angwaye
Wadanda suka yi mutuwar fuju'a
Asali: UGC

5. Bolade Olwuatobi

A watan Mayun 2021, labarin Bolade Olwuatobi ya ratsa ko ina. Wannan Lauya ta rasu ne bayan ta auri mijinta, Adebayo Oluwatayo da ke zama a Amurka.

6. John Abugu

Shi kuwa John Abugu ya mutu ne a sakamakon hadarin mota da ta rutsa da shi. Toyota Hilux ta murje matashin a garin Ikyangedu, ana shirin daura masa aure.

7. Vivian

Akwai wata Amarya mai suna Vivian wanda ta rasu a ranar 19 ga watan Yuli, 2021. Wannan budurwa ta rasu ne kwana daya bayan daura mata aure, kafin ta tare.

8. Aisha Kabir

A lokacin da ake shirin auren Aisha Kabir da Malam Shahrehu Alhaji Ali, sai uwargidar wannan mutumi ta yi kutun-kutun ta kashe wanda ake shirin zai aura a Kano.

9. Sulaiman Abdullahi

A Oktoban 2021, wani saurayi Sulaiman Abdullahi ya yi mutuwar fuju’a. Sulaiman ya rasu ne a inda yake aiki, asibitin jami’ar ABU Zaria, ana saura watanni aurensa.

Kara karanta wannan

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

10. Chiamaka Emmanuel

Kwanaki Nairaland ta kawo labarin Chiamaka Emmanuel da aka samu gawarta tare da wani Steven Ayika. Emmanuel ta mutu bayan an sa mata ranar aure a Disamba.

11. Sani Ruba

A watan Nuwamban nan ne aka ji mutuwar Sani Ruba a hadarin mota a hanyar Yola. Ruba ya rasu ne ana saura makonni uku aurensa da Rafeeah Zirkarnain a Zaria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel