Gyara Kimtsi: An nada ministan Buhari, Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi

Gyara Kimtsi: An nada ministan Buhari, Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi

  • Mai Martaba Sumaila Mera, sarkin Argungun, ya nada Alhaji Lai Mohammed sarautar kakakin Kebbi
  • An yi bikin nadin sarautar ne a ranar Lahadi a fadar basaraken da ke jihar Kebbi daga cikin bikin ranar shakatawa
  • Basaraken ya ce an bai wa ministan al'adun sarautar ne ganin yadda ya ke bada gudumawa ga al'adun kasar nan

Kebbi - Sarkin Argungun, Mai Martaba Sumaila Mera a ranar Lahadi ya bai wa ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi, Daily Trust ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa an yi nadin sarautar a cikin fadar sarkin Argungun da ke jihar Kebbi duk daga cikin jerin shagalin ranar shakatawa da za a yi a Birnin Kebbi ranar Litinin.

Gyara Kimtsi: An nada ministan Buhari, Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi
Gyara Kimtsi: An nada ministan Buhari, Lai Mohammed sarautar Kakakin Kebbi. Hoto daga @bbchausa
Asali: Instagram

A yayin jawabi wurin bikin, sarkin ya ce an bai wa ministan wannan sarautar ne saboda kwazonsa wurin karfafa kyawawan tsarin al'adun Najeriya a gida da waje.

Kara karanta wannan

Kungiyar CAN Ta Karrama Wani Limami Akan Ceton Kiristoci 200 Da Ya Yi a Plateau

Sarkin ya ce masarautar ta karrama ministan da wannan sarautar ne a matsayin hanyar nuna godiya kan kokarinsa na karfafa wa da kawo cigaban gasar kamun kifi ta Argungun yadda duniya za ta san da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NAN ta ruwaito cewa, gasar kamun kifi ta Argungun a 2017 wacce ta samu 'yan kallo a gida da kasashen ketare, UNESCO ta kwatanta shi da al'ada mai matukar amfani.

Sarkin ya kara da jinjina wa ministocin da suka gabata kan kokarinsu wurin inganta bikin tun daga 1970, Daily Trust ta wallafa.

"A al'adance, Kakaki wani abu ne da ake amfani da shi wurin jawo hankula. Daga sarki har zuwa jama'ar masarautar, an mika sarautar nan ga mai ita."

Sojin Najeriya sun dakile farmakin da ISWAP suka kai sansanin soji da wasu yankunan Yobe

A wani labari na daban, a yammacin ranar Alhamis ne dakarun sojin Najeriya su ka yi nasarar dakile wani farmaki da 'yan ta'addan Islamic State of West Africa Province (ISWAP) suka kai sansanin soji da kuma wasu yankuna na jihohin Borno da Yobe.

Kara karanta wannan

Datse sadarwa: 'Yan bindiga na amfani da layikan Nijar wurin kai farmaki, Dan majalisa

PRNigeria ta gano cewa, dakarun dauke da manyan makamai sun bankado yunkurin harin da miyagun 'yan ta'addan suka kai Malam Fatori da ke jihar Borno.

'Yan ta'addan da suka bayyana a motocin yaki da babura, zakakuran dakarun sun fi karfinsu inda suka batar da wasu daga ciki yayin da wasu suka ja da baya tare da tserewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: