Kano: Kotun shari'ar musulunci ta umurci a bawa matashin da ya saci hula 6 da turare masauki a gidan yari

Kano: Kotun shari'ar musulunci ta umurci a bawa matashin da ya saci hula 6 da turare masauki a gidan yari

  • Alkalin kotu kotun shari'a a Kano ya bada umurnin a bawa wani matashi Aminu Bashir masauki a gidan gyaran hali
  • Hakan ya biyo bayan gurfanar da matashin ne aka yi bisa zarginsa da kutse tare da sace tufafi, huluna shida da kwalban turare
  • Wanda aka gurfanar ya amsa laifinsa hakan yasa Alkalin kotun Dr Bello Khalid ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Janairu

Kano - Wata kotun shari'ar musulunci mai zamanta a Fagge, a ranar Laraba ta bada umurnin a ajiye mata wani matashi mai shekaru 20, Aminu Bashir, a gidan gyaran hali, bayan amsa cewa ya saci hula shida, kwalbar turare da tufafi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan sanda sun gurfanar da Bashir, mazaunin Sharada NNDC Quaters a Kano ne da laifin kutse da sata.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Kano: Kotun shari'ar musulunci ta umurci a bawa matashin da ya saci hula 6 da turare masauki a gidan yari
Kotun shari'a a Kano ta bada umurnin a ajiye mata wani da ya saci hula, turare da tufafi. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin kotun, Dr Bello Khalid, ya bada umurnin a ajiye Bashir a gidan gyaran hali kafin yanke masa hukunci, ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Janairu.

Yadda lamarin ya faru

Tunda farko, mai gabatar da kara, Mr Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Disamba a Sani Mainage Quarters, Kano, Daily Trust ta ruwaito.

Wada ya ce misalin karfe 7.10 na dare ne, wanda aka yi karar ya kutsa gidan wani Zulyadini Muhammad ya sacemasa huluna shida, tufafi da turare da kudinsu ya kai N96,000.

Ya ce an kwato kayayyakin daga hannun wanda aka yi karar sannan laifin ya ci karo da tanade-tanaden sashi na 213, 133 da 201 na Dokar Shari'a ta Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

A wani labarin, an kama wani mai aiki a wurin wankin mota a Kano, Abdullahi Sabo, saboda tsere wa da motar kwastoma da aka kawo masa wanki, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Daura, Jihar Katsina da motar na sata.

Mr Kiyawa ya ce, a ranar 30 ga watan Nuwamba, yan sanda sun samu korafi daga wata mazauniyar Badawa Quaters a Kano inda ta ce wani mai aiki a wurin wankin mota ya gudu masa da motarsa Honda Accord ta shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel