Za mu zo lokacin bikin Kirsmeti: ISWAP ta rubuta wa wasu garuruwan Adamawa wasiƙa

Za mu zo lokacin bikin Kirsmeti: ISWAP ta rubuta wa wasu garuruwan Adamawa wasiƙa

  • ISWAP ta tura wasiku inda ta yi barazanar kai farmaki wasu garuruwa da ke karkashin karamar hukumar Machika a jihar Adamawa cikin kwanakin bikin kirsimeti
  • Mazauna garin Bazza da ke karamar hukumar sun tabbatar da ganin wasikun da safiyar ranar Laraba inda aka ajiye su wuri-wuri a cikin babban titin garin
  • Mazaunan sun bayyana yadda tsoro ya ratsa zukatan jama’a da dama inda su ka dinga tururuwar zuwa karanta wasikun da kuma gani da idanunsu

Jihar Adamawa - Kungiyar 'yan ta'adda ta ISWAP ta yi barazanar kai farmaki wasu garuruwa da ke karkashin karamar hukumar Machika a jihar yayin bikin kirsimeti da ke karatowa, Arise Tv ta ruwaito.

Mazauna Bazza a Machika, sun tabbatar da karanta wasikun da ‘yan ta’addan su ka tura wadanda su ka gani a kan babban titin garin ranar Laraba da safe.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Za mu zo lokacin bikin Kirsmeti: ISWAP ta rubuta wa wasu garuruwan Adamawa wasiƙa
ISWAP ta yi barazanar kai wa wasu mazauna Adamawa hari yayin bikin Kirsimeti. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda mazaunan su ka shaida, wadannan wasikun sun janyo tashin hankali da damuwa ga mazauna garin inda su ka dinga tururuwar zuwa karanta wasikun.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“An ajiye wasikun ne a wasu garuruwan inda su ke sanar da shirin ‘yan ISWAP na kai farmaki a ranar kirsimeti.”

Ana kyautata zaton mayakan ne su ka ajiye wasikun

Shehu Kambile, wanda mazaunin Machika ne ya tabbatar wa da manema labarai ganin wasikun a Yola ta wayar salula, ya ce ana zargin mayakan ISWAP ne su ka ajiye wasikun a Bazza da wasu garuruwan da ke Machika.

Kamar yadda ya shaida:

“Yan ta’addan sun ja kunne inda su ka lashi takobin kai farmaki garuruwanmu lokacin shagulgulan kirsimeti.
“Yanzu haka mutanenmu cikin tashin hankali su ke saboda sun san yadda ‘yan ta’addan su ke cika duk wata barazana da su ka yi.

Kara karanta wannan

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

“Idan hakan ya faru, sai mun shiga damuwa sakamakon yadda ake cikin tsananin rayuwa a kasar nan.”

Ya kara da fatan sojoji da sauran jami’an tsaro za su yi binciken sirri don dakatar da ko wacce kafar ta’addanci.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ya ce bai san da labarin wasikun ba

Manema labarai sun nemi jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda, DSP Suleiman Nguroje, inda ya ce bai san komai ba dangane da wasikun.

Amma ya yi alkawarin kira idan ya tattauna da DPO din anguwannin da lamarin ya shafa ta waya.

Sai dai har lokacin da Arise Tv ta ke rubuta wannan rahoton, kakakin rundunar ‘yan sandan bai kira ba.

Brigade Commander, 23 brigade Yola, Birgediya Janar Aminu Garba ya ce ba karkashin ikonsa yankin ya ke ba.

A cewarsa:

“Ku yi magana da Commander 28 Brigade Chibok. Ba a karkashin iko na su ke ba. Batun wasikokin nan ya fara ta’azzara, su kuskura su zo su gani idan za su koma.”

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai

A wani labarin mai alaka da wannan, Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojoin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.

Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.

Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel