Bidiyon Gwamnan Najeriya da tauraron BBN, Whitemoney suna girki ya ɗauki hankalin mutane

Bidiyon Gwamnan Najeriya da tauraron BBN, Whitemoney suna girki ya ɗauki hankalin mutane

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu da Whitemoney sun dauki hankali a taron shagalin girke-girken jihar Legas na shekarar 2021 ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba
  • An ga gwamnan a wani bidiyo su na girki tare da Whitemoney, wanda ya ci nasara a shirin gidan talabijin din BBNaija na shekarar 2021
  • Tuni mutane su ka fara surutai iri-iri inda su ke zargin cewa salon kamfen ne gwamna ya ke yi yayin da zaben 2023 ya ke kara matsowa

Jihar Legas - Wani bidiyo ya nuna gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya na girki tare da Hazel Onoduenyi, wanda aka fi sani da Whitemoney, ya janyo surutai a kafafen sada zumunta.

A bidiyon an ga gwamna Sanwo-Olu tare da Whitemoney, wanda ya ci nasara a shirin gidan talabijin na BBNaija shekarar 2021, sanye da bakaken rigunan girki su na girki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnan APC ya lashi takwabi, ya ce shi da APC mutu ka raba

Bidiyon Gwamnan Sanwo-Olu da Whitemoney suna girki a wurin bikin girke-girke ya dauki hankalin mutane
Hoton gwamnan Legas suna girki tare da Whitemoney. Photo credit: GreaterLagos/Punch Newspapers
Asali: Instagram

Yayin da aka hango gwamnan ya na juya abinci yayin da Whitemoney ya ke zuba magi a cikin abincin inda mutane su ka dinga kallonsu cike da burgewa.

An yi shagalin bikin abinci na jihar Legas na shekarar 2021 ne a Muri Okunola Park da ke Victoria Island a cikin jihar Legas, mai taken “A Taste of Lagos”.

Shagalin, kamar yadda kwamishinan noma, Ms Abisola Olusanyato, ya ce zai sa ‘yan kasuwan ciki da wajen kasa su yi sha’awar siyan kayan abincinmu.

Abinda na girka a shagalin girke-girken jihar Legas - Gwamna Sanwo-Olu

Yayin da gwamna Sanwo-Olu ya yi wata wallafa da a shafinsa na Facebook ya ce ya taya bakon da su ka gayyata ya yi girki a shagalin, Whitemoney.

Kara karanta wannan

Kafin a birne shi, ‘Yan Sanda sun samu wani da hannu a kashe Kwamishinan Katsina

Sun yi wani girki ne wanda aka yi amfani da albasa, sannan aka gasa kifi iri-iri aka hada yaji da magi da sauransu.

Ya kara da cewa:

“Ma’aikatar noma ce ta shirya Shagalin girke-girken don bayyana abubuwan da jihar Legas ta ke hadawa don nuna wa ‘yan kasuwa har na kasashen waje.
“Ina ba ‘yan kasuwa kwarin guiwa akan yin amfani da damar Lagos State Employment Trust Fund (LSETF) don bunkasa kasuwancinsu, inda ya kula da yadda aka yi amfani da shagalin wurin tallafa wa sana’o’i.
“Gwamnatinmu ta jajirce wurin tallafa wa kananun sana’o’i, manya da matsakaita (MSMEs) kuma za mu dage wurin ci gaba da gyara akan kasuwanci a Legas.”

Tsokacin jama’a karkashin bidiyon

Ogbonnaya Stephen ya yi tsokaci a Facebook inda ya ce:

“Wannan abincin da mutane biyu ke girkawa, ina fatan kada a yi kuskure. Ina son gwamna Sanwo-Olu, ba ya da girman kai. Ya na kula matasa duk inda ya gansu. Ba ya da jin kai.

Kara karanta wannan

Ana yi wa Shugaban kasa martani a kan zuwa Legas, ana makokin mutum 80 a Sokoto

“Ka kyauta Odogbu Whitemoney saboda tsayawa inda kake. Ka ji dadinka!”

Victor Rossoneri Muodufor yace:

“Gwamna Sanwo-Olu ya na da wayau.
“Yana amfani da wannan salon don shigewa zuciyarku.”

Oluyemi Abiodun ya ce:

“Kawai gwamnan ya na amfani da damar nan ne don ya yi borin kunya. Gwamnan da ya bayar da damar a yi ta harbe-harbe a lekki toll gate. Mu na bukatar amsa.”

Princess Adebisi Gbadebo Adeleke ya ce:

“Wannan salon yin kamfen na 2023 ne.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel