Nasara daga Allah: Sojoji sun hallaka mayakan Boko Haram, sun kwato manyan makamai a Adamawa
- Rundunar sojin ƙasa ta bayyana yadda dakarunta suka yi wa yan ta'adda kwantan bauna a jihar Adamawa
- Sojojin sun yi musayar wuta da yan ta'addan, inda suka hallaka wasu, kuma suka kwato manyan makamai
- Kwamandan sojojin ya yaba da wannan nasara da jami'an suka samu saboda jajircewarsu da kwarin guiwarsu
Adamawa - A ranar Talata, rundunar sojin ƙasa ta bayyana cewa ta kashe mayaƙan Boko Haram 6 a wata musayar wuta a ƙauyen Sabon Gari, ƙaramar hukumar Madagali, jihar Adamawa.
Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo, kwamandan runduna ta 7 shine ya bayyana haka a wata hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN).
Vanguard ta rahoto Eyitayo na cewa dakarun Operation Haɗin Kai, sune suka samu wannan nasarar yayin ɗaukar mataki bayan samun bayanan sirri kan yan ta'addan.

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa gwarazan sojojin sun yi wa yan ta'addan kwantan bauna suka bude musu wuta, inda suka hallaka shida daga cikinsu yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi a jikinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace:
"Dole tasa yan ta'addan suka tsere da gudu zuwa kan hanyar Lemu, yayin da sojojin ba su ƙyale su ba, suka biyo baya suka hallaka wasu."
Sojojin sun kwato manyan makamai
Eyitayo ya kuma bayyana cewa dakarun sojin sun kwato motocin yaƙi biyu, bindigun kakkaɓo jirgin sama guda biyu, bindigu kirar AK-47 hudu, da Magazine guda hudu.
Kwamandan ya yaba wa sojijin na bataliya ta 144 bisa namijin kokarin da suka yi da kuma jajircewar su.
A cewarsa jami'an sojin sun mamaye lungu da sako na yankin da sintiri domin tabbatar da cewa an fatattaki yan ta'adda baki ɗaya.

Kara karanta wannan
Karin bayani: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da sarakuna biyu, sun ƙone fadarsu da motocinsu
A wani labarin na daban kuma EFCC ta bankaɗo Yadda wani gwamna a Arewa ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa
Hukumar EFCC tace sabon sashin da ta kirkiro na fasaha ya fara aiki, domin zuwa yanzun ya gano wasu bayanan sirri.
Hukumar tace ɗaya daga cikin abubuwan da sashin ya bankado shine yadda wani gwamna ya cire kudi daga lalitar jiharsa.
Asali: Legit.ng