An cinna wa ɗalibin mu wuta da ransa saboda ya ƙi shiga ƙungiyar asiri, UNIOSUN

An cinna wa ɗalibin mu wuta da ransa saboda ya ƙi shiga ƙungiyar asiri, UNIOSUN

  • Jami'ar Jihar Osun, UNIOSUN ta tabbatar da cewa wasu yan kungiyar asiri ne suka kai wa wani dalibinta hari
  • Binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa yan kungiyar asirin sun kai wa dalibin hari ne saboda ya ki yarda ya shiga kungiyarsu
  • Sun kai masa hari da adduna da duwatsu suka masa rauni sannan suka cinna masa wuta suka yi gaba amma mutane suka cece shi

Osun - Mahukunta a Jami'ar Jihar Osun, Osogbo, sun ce jami'an tsaron su na aiki da yan sanda domin ganin an kama yan kungiyar asirin da suka kai wa dalibi, Victor Oke, hari a Akede, Osogbo, a ranar Asabar don a hukunta su, rahoton Punch.

An cinna wa ɗalibin jami'a wuta da ransa saboda ya ƙi shiga ƙungiyar asiri, UNIOSUN
An cinna wa ɗalibi wuta da ransa saboda ya ƙi shiga ƙungiyar asiri, UNIOSUN. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Sanarwar da mai magana da yawun jami'ar, Ademola Adesoji ya fitar a Osogbo, a ranar Litinin, ta yi bayanin cewa, an yi kokarin tilasta wa dalibin shiga kungiyar asiri ne amma ya ki.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu

Adesoji ya ce dalibin bai samu zuwa rubuta jarabawarsa ta karshe ba a ranar Asabar, da kuma aka tuntubi iyayensa sai aka gano cewa yan kungiyar asiri ne suka kai masa hari.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An gano cewa wasu mutane da ke yankin inda abin ya faru sun kai rahoto bayan sun ji Oke Ademiju Victor yana ihu yana cewa ba zai shiga kungiyar asirinsu ba, a yayin da suke cigaba da sararsa da adda, manyan duwatsu sannan suka yi yunkurin kona shi, sun kona wasu sassan jikinsa kafin aka cece shi.
"Muna cigaba da tuntubar iyayensa kuma mun tabbatar cewa an garzaya da shi zuwa asibitin koyarwa na jami'ar domin bashi kulawa sannan daga baya aka mayar da shi zuwa wani asibitin da ba a bayyana ba domin cigaba da masa magani."

Punch Metro ta ruwaito cewa wasu yan kungiyar asiri ne suka kai masa hari suka cinna masa wuta suka bar shi ya mutu amma mazauna yankin suka kawo masa dauki.

Kara karanta wannan

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe

A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.

Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel