Da Dumi-Dumi: An Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu

Da Dumi-Dumi: An Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu

  • Wasu bata gari da ake zargin yan fashi da makami ne sun kashe hamshakin dan kasuwan Najeriya, Olusola Solarin a kasar Afirka ta Kudu
  • Rahotanni sun bayyana yadda yan fashin suka shiga shagonsa suka sace kudi, wayar salula da wasu kayayyaki kafin suka fita da shi suka bindige shi
  • Rundunar yan sanda a kasar ta Afirka ta Kudu ta fara bincike a kan kisar amma kawo yanzu ba a riga an kama kowa ba bisa zargin kisar

Afirka ta Kudu - Wasu 'yan bindiga da ba a riga an gano ko su wanene ba sun bindige fitaccen dan kasuwa Olusola Solarin daga jihar Ogun a Pretoria, kasar Afirka ta Kudu.

SaharaReporters ta gano cewa marigayin shine mijin Doris Ikeri-Solarin, wacce aka zaba matsayin mataimakiyar yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da sarakuna biyu, sun ƙone fadarsu da motocinsu

Da Dumi-Dumi: An Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu
Yan Fashi Sun Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

An rahoto cewa an kai masa hari ne a shagonsa a ranar Lahadi.

Majiya ta shaidawa SaharaReporters cewa:

"An ritsa Sola a shagonsa ne, bai yi kakawa da yan fashin ba. Amma bayan sun masa sata, sai suka bukaci ta bi su daga nan kuma suka bindige shi har lahira."
"Sola ne mijin Doris Ikeri-Solarin wacce a baya-bayan nan aka nada mataimakiyar shugaban kungiyar yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu. Kawo yanzu yan sanda ba su kama kowa ba."

Matarsa, Ikeri-Solarin kuma shine direktan, DIDA Clothiers, a cewar bayanan da ta wallafa a Linkedln.

Adetola Olubajo, tsohon shugaban kungiyar yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu ya shaidawa SaharaReporters cewa lamari ya faru ne misalin karfe 5 na yamma.

Ya ce:

Kara karanta wannan

'A jami'ar BUK na fara haɗuwa da shi', Matar kwamishinan da aka kashe a Katsina ta magantu

"Ni ne farkon zuwa wurin domin ni na kai matarsa wurin. Da muke gidansa an kira mu cewa yan fashi sun kai hari a shagonsa. Sunan unguwar Highway Park, babu nisa daga wani fitanannen unguwa mai suna Tembisa.
"Yan daba sun shiga shagon, sun sace kudi da wayoyin salula sannan suka fita da shi wajen shagon. Suke harbe shi. Abin da ganau suka fada mana kenan.
"Mun gana da yan sanda amma ya ce jiya aka ba shi rahoton don haka zai fara bincike a yau. Abin da muka sani kenan kawo yanzu."

Mutuwar Olusola na zuwa ne watanni bayan mutuwar wani dan Najeriya, Okechukwu Henry, dan jihar Imo kamar yadda Ben Okoli ya sanar, Shugaban Kungiyar Yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu.

Wasu yan fashi da ba a san ko su wanene ba suka daba wa Henry wuka hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel