Babbar magana: Wata mata ta rasa aikinta saboda tsananin yin 'Bleaching'

Babbar magana: Wata mata ta rasa aikinta saboda tsananin yin 'Bleaching'

  • Wata mata ta rasa aikinta saboda kodar da fatar jikinta da kuma zama mai launin fata iri biyu, lamarin da uwar dakinta ta ce bata lamunta ba
  • Uwar dakin tace koran ya zama dole saboda matar ta yi bilicin har fatarta ta yi fari yayin da yatsunta suka yi baki kirin
  • A ra'ayin uwar dakin nata, wai bai kamata kwastomomi su ga jikinta da hannayenta na da bambanci ba, hakan zai iya korar su

Wata 'yar Najeriya mai suna Ikot Sharon ta ba da labarin yadda wani gidan cin abinci ya bai wa wata ma’aikaciya takardar kora saboda bilicin da rashin daidaito a launin fatarta.

Da take ba da labarin dalilin da yasa aka kori matar a shafin Twitter, @IkotSharon ta ce fatar ma'aikaciyar ya yi muni wanda ya haifar da duhun kullin hannayenta wanda ya bambanta da farar fatarta.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano zai angwance da galleliyar budurwa, tsohuwar zumansa nan kusa

Matar da tayi bilicin
Yadda wata mata ta rasa aikinta saboda sauya launin fatarta daga baka zuwa fara | Hoto: Sharon Ikot/Twitter
Asali: Twitter

Wani bangare na rubutun Twitter din yana cewa:

"Haka wata mata aka koreta yau saboda tayi bilicin sosai, kullin hannayenta sunyi duhu yayin da jikinta yayi fari."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba za ta iya yi wa baki hidima da yadda hannayenta suke ba, dole ta tafi

Bisa wannan rashin daidaiton launin fata, an nuna wa ma’aikaciyar kofar fita domin a cewar uwar dakinta, ba zai yiwu ta iya hidimtawa baki da kodadden jiki tare da kullin hannu mai rodi-ridi.

"Tabbas ba za ta iya yiwa baki hidima da wadancan hannayen ba don haka dole ne mu kore ta."

Ba na adawa da yin bilicin

Lokacin da wasu daga cikin mabiyanta suka nuna rashin amincewarsu kan matakin da aka dauka na ladabtarwa, ta kare matakin da ta dauka tana mai cewa an baiwa ma’aikaciyar damar sanya safar hannu ko kuma a kore ta amma taki.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

"Bana adawa da kodar da fatar jikinki amma dai kiyi shi dai dai, ba ma nuna bambanci ga ma'aikata da kowane irin sharudda, mun yanke shawarin korar ta ne saboda korafe-korafen da ake samu na rashin tsabta, ta ki yarda."
"Safar hannu ma zabi ne a gare ta. Muna gudanar da binciken lafiya akan duk ma'aikatanmu kuma muna nemo mafi kyawun hanyoyin sarrafa su tare da mu.
"Mun yi yadda zamu fitar da ita daga wurin amma ta ki saboda an dauke ta a matsayin “waitress”. Ba mu kyale ta ta tafi ba tare da kokarin yin tunani akanta ba kuma mun yi la'akari da sha'awar kwastomominmu."

Kodar da fata al'ada ce da ta mamaye tsakanin mata masu duhu. Rahoton Fabrairu 2021 na The Conversation ya nuna cewa mata masu duhun launin fata suna kashe kusan dala biliyan 8.6 kowace shekara don yin bilicin fata.

Jigon gwamnati ya bayyana yadda kyankyaso mai rai ya zauna a kunnensa na tsawon watanni

Kara karanta wannan

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

A wani labarin, sabon sakataren din-din-din na ma’aikatar ciniki da kasuwanci a Anambra, Samuel Ike, ya bayyana godiyarsa ga Allah da ya ceci rayuwarsa ta hanyar sauko masa da mu’ujiza.

Ike wanda ya yi magana a cocin St. James Anglican a hidimar godiya a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba, kan ikon Allah, ya ba da labarin yadda wani kwaro, kyankyaso ya kutsa cikin kunnensa ya zauna na tsawon watanni kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Tribune ya kara da cewa sabon sakarataren na din-din-din ya ce wani likita ya shaida masa cewa zai haukace idan da kwaron ya shiga cikin kwakwalwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel