Gwamnatin tarayya ta umarci a cire Tireloli daga kan hanyar Abuja-Kaduna-Kano

Gwamnatin tarayya ta umarci a cire Tireloli daga kan hanyar Abuja-Kaduna-Kano

  • Gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin da take ganin zai rage cunkoson ababen hawa da saukake amfani da hanyar Abuja-Kaduna-Kano
  • Gwamnati ta kafa kwamiti na musamman domin kawad da Tireloli da sauran manyan motoci a kan babban hanyar
  • Daraktan sashin gina hanyoyi, Injiniya Esan, yace gwamnati zata samar da wurin ajiye motoci na wucin gadi

Abuja - Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin haɗin guiwa tsakanin hukumomi domin kawad da Tireloli daga kan hanyar Abuja-Kaduna-Kano.

Leadership ta ruwaito cewa gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne domin rage cunkoson ababen hawa dake kan hanyar da kuma lalacewar hanya.

Daraktan sashin gina manyan hanyoyi da gyarasu na ma'aikatar ayyuka, wanda shine shugaban kwamitin, Injiniya Folorunsho Esan, shine ya faɗi lokacin da ya kai ziyarar duba hanyar.

Manyan motoci
Gwamnatin tarayya ta umarci a cire Tireloli daga kan hanyar Abuja-Kaduna-Kano Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Esan ya bayyana cewa ma'aikatarsu zata samar da wurin aje motocin na wucin gadi a Tafa, kan hanyar Kaduna, inda Tirelolin zasu iya fakin.

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi na tura wa 'yan NEPA karnuka yayin da suka zo yanke wuta

Ya ƙara da cewa wurin ajiye motocin zai ɗauki Tireloli 500, da zaran ya fara aiki, wanda hakan zai saukake cunkoso da matsalar tsaron dake yankin.

Meyasa FG ta kafa kwamitin?

A cewar Esan, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, shine ya kafa kwamitin bisa umarnin shugaban ƙasa, domin kawad da manyan motocin daga wannan babbar hanya.

Ya kuma bayyana cewa ya zo wannan ziyarar ne domin ganin inda Tirelolin ke ajiye da kuma wurin da ya kamata a maida su, su bar kan hanyar.

A jawabinsa yace:

"Hakan zai saukaka wa masu bin hanyar don zasu wuce cikin sauki. Mun zo nan ne domin diba wuraren da ya dace a maida Tirelolin."

Ko ya direbobin suka ji da wannan mataki?

Wakilin kungiyar Tankokin dake dakon man fetur, Abdullahi Haruna, yace direbobin Tanka a shirye suke su cika umarni da zaran gwamnati ta samar da wurin aje motocin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta bude layukan sadarwa a kananan hukumomi 17 na jihar

"Mu, direbobin Tankoki, mun shirya baiwa kwamiti goyon baya wajen kawad da manyan motoci daga kan hanya."
"Abinda muke bukata shine wurin ajiye motocin na wucin gadi ayi shi da inganci, babu bukatar a yi na dindindin, wannan ma ya isa."

A wani labarin kuma Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da sarakuna biyu, sun ƙone fadarsu da motocinsu

Da safiyar Lahadi, wasu tsagerun yan bindiga suka kaddamar da mummunan hari kan kauyukan jihar Imo,.inda suka sace sarakuna biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ƙone fadar sarakunan da suka sace da motocin su na hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel