Matar da tace tana kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiyarta da 'ya'ya 4 ta rasu

Matar da tace tana kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiyarta da 'ya'ya 4 ta rasu

  • Bayan jinyan kwana biyu a asibiti, daya daga cikin wadanda suka sha a harin Sokoto ta rasu
  • Gabanin rasuwarta, a gaban idanunta ‘yan bindigan su ka kona mahaifiyarta, yaranta hudu da kuma wasu ‘yan uwanta har su ka zama toka
  • Shugaba Buhari ya tura tawaga jihar Sokoto don jajantawa iyalan mamatan

Sokoto - Shafa'atu, matar da ta tsallake rijiya da baya a harin da yan bindiga suka kaiwa matafiya a Sokoto kuma ta rasa yan'uwanta guda rasu ta rigamu gidan gaskiya.

Matar ta mutu ne a asibitin koyarwan jami'ar Danfodio dake Sokoto inda take jinyan raunukan da ta samu a harin.

Daily Trust ta ruwaito cewa an yi jana'izar Shafa'atu bisa koyarwan addinin Musulunci.

Matar da tace tana kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiyarta da 'ya'ya 4 ta rasu
Matar da tace tana kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiyarta da 'ya'ya 4 ta rasu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bayan Ƙona Fasinjoji Da Ransu, Ƴan Bindiga Sun Sake Zubar Da Jini a Wani Gari a Sokoto

Gabanin rasuwarta, Shafa’atu, ta shaida cewa ita da yaranta, mahaifiyarta, kaninta, da yaran ‘yan uwanta su na cikin motar a wuraren titin Sabon Birni-Isa lokacin da ‘yan bindiga su ka kai musu farmaki.

Ta ce akwai manya 33 da yara da dama a cikin motar

A cewarta, a cikin motar akwai manya 33 da yara da yawa lokacin da ‘yan bindigan da ake zargin yaran Bello Turji, ‘yan bindigan da su ka addabi arewacin Sokoto, ne su ka kai musu farmakin.

Kamar yadda ta shaida:

“Sun dinga harbin motar mu har sai da ta mulmula sau uku sannan ta kama da wuta. Cikin hukuncin Ubangiji daga ni sai wani fasinja ne mu ka tsira amma duk sauran sun mutu saboda harbin da ya same su.
“Na rasa yara na hudu, uku duk sun girma da kuma jariri mai watanni goma. Ina kallonsu har da mahaifiyata, kawuna da yaran yayyina duk su ka kone kurmus yayin da ‘yan bindigan su ke kallonmu cike da nishadi.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel