Sojoji sun ceto 'yan sanda 20 da 'yan ISWAP da Boko Haram suka yi garkuwa dasu a Yobe

Sojoji sun ceto 'yan sanda 20 da 'yan ISWAP da Boko Haram suka yi garkuwa dasu a Yobe

  • Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, an ceto wasu jami'an 'yan sanda daga hannun 'yan ta'adda
  • A baya dai an sace 'yan sandan ne a wasu yankunan Yobe, inda suke hannun 'yan ta'addan da ke addabar yankin
  • An ceto su, tare da fatattakar 'yan ta'adda masu yawa, tare da hallaka wasu daga cikin 'yan ta'addan da dama

Yobe - Hedkwatar tsaro ta sanar da cewa, an ceto 'yan sanda 20 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai wa sashen 'yan sanda da ke Buni Yadi a garin Buni Yadi.

Mukaddashin daraktan harkokin yada labarai na rundunar Birgediya Janar Benard Onyeuko, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan soji da ke gudana a cikin makwanni biyun da suka gabata ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Mun san wasu yan Boko Haram da suka mika wuya tuban muzuru sukayi, Kwamandan Operation Hadin Kai

Taswirar jihar Yobe
Da dumi-dumi: An ceto 'yan sanda 20 'yan ta'adda suka yi garkuwa dasu a Yobe | Hoto: newnow.ng
Asali: UGC

Ya kuma ce sun fatattaki ‘yan ta’addan daga sansanoninsu yayin da wasu suka mika wuya, The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, a cikin lokacin da ake magana, an kashe jimillar ‘yan ta’adda 62 tare da kama 28.

Punch ta ruwaito shi yana cewa:

“A dunkule, an kashe ‘yan ta’adda 62, sannan an kama 28 daga cikinsu, sannan an kwato makamai iri-iri 54 da alburusai 144 daban-daban.
"Haka kuma, an kwato jimillar dabbobi 101 da aka sace, da kuma jami’an NPF 20, wadanda aka yi garkuwa da su a lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari a ofishin ‘yan sanda, sojoji Buni Yadi sun kubutar da su a cikin wannan lokaci.”

Mafarauta sun kame 'yan bindiga 3 bayan doguwar musayar wuta

An kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a maboyar su da ke kusa da unguwar Ossra-Irekpeni da ke kan titin Okene zuwa Lokoja zuwa Abuja.

Kara karanta wannan

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

Daya daga cikin mafarautan yankin da suka kai harin ya shaida wa Daily Trust cewa an yi musayar wuta dasu.

Ya ce mafarautan tare da shugaban karamar hukumar Adavi ta jihar Kogi, Joseph Samuel Omuya, sun kai farmaki dajin ne bisa samun rahoton kasancewar 'yan ta'addan a yammacin Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel