Mun san wasu yan Boko Haram da suka mika wuya tuban muzuru sukayi, Kwamandan Operation Hadin Kai

Mun san wasu yan Boko Haram da suka mika wuya tuban muzuru sukayi, Kwamandan Operation Hadin Kai

Abuja - Babban jami'in hukumar Sojin Najeriya ya bayyana cewa sun san akwai wasu yan ta'adda da suka mika da ba da gaske suke ba kuma suna yiwa yaki da Boko Haram zagon kasa.

Manjo Janar Christopher Musa ya bayyana cewa amma hakan ba ya nufin babu alkhairi a mika wuyan da sukeyi.

A cewarsa, idan akayi abinda ya dace dasu, za'a ga karshen ta'addancin Boko Haram nan ba da dadewa ba.

Kwamandan Operation Hadin Kai
Mun san wasu yan Boko Haram da suka mika wuya tuban muzuru sukayi, Kwamandan Operation Hadin Kai Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Janar Christopher wanda shine Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai dake Borno ya bayyana hakan ne a taron shugaban hafsan Sojin kasa a Abuja

Ya ce babban kalubalen dake gabansu yanzu shine abinda za'a yi da tubabbun yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a

A cewarsa:

"Mun samu sama da mayaka 20,000 da iyalansu da suka mika wuya. Hakan na nufin cewa muna samun nasara. Abinda zamu yi dasu nan gaba shi ke gabanmu. Abinda mukayi zato shine bayan mika wuyar za'a ga karewar yakin, amma abin ba haka yake ba."
"Lallai akwai wasu da tuban gaske sukayi, amma ba zamu ce babu masu tuban muzuru ba, da suke da wata manufa ta daban."
"Kamar yadda na fada, idan muka yi abinda ya dace da su, da yiwuwan mu fara ganin karshen ta'addanci nan kusa."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel