Buhari: Dalilan da suka sa rashin tsaro ba zai hana masu zuba hannayen jari zuwa Najeriya ba

Buhari: Dalilan da suka sa rashin tsaro ba zai hana masu zuba hannayen jari zuwa Najeriya ba

  • Shugaban kasa ya kare matakin da Najeriya ta ke a wani jerin matakin masu zuba hannayen jari da bankin Rand Merchant ya wallafa
  • Najeriya ta bayyana a mataki na 14 a jerin sunayen kasashen da masu zuba hannayen jari a Afrika ke tururuwar zuwa a 2021
  • Shugaban kasan ya soke hakan inda ya musanta tare da yin ikirarin cewa har yanzu Najeriya ce wurin da ya fi ko ina jan hankalin masu zuba hannayen jari

Fadar shugaban kasa ta kara jaddada cewa Najeriya har yanzu ita ce kasar da ta fi dacewa masu zuba hannayen jari a Afrika su yi tururuwar zuwa duk da kalubalen tsaro.

Femi Adesina, mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da Channels TV.

Kara karanta wannan

Akwai Abin Tsoro Da Takaici A Kasar Nan, Malamai dai sun yi nasu kokarin: Dr Rabiu Rijiyar Lemo

Buhari: Dalilan da suka sa rashin tsaro ba zai hana masu zuba hannayen jari zuwa Najeriya ba
Buhari: Dalilan da suka sa rashin tsaro ba zai hana masu zuba hannayen jari zuwa Najeriya ba. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

Kamar yadda yace, duk da kalubalen tsaron da ke addabar Najeriya wanda ya hada da Boko Haram, rikicin makiyaya da garkuwa da mutane, ba zai hana masu zuba hannayen jari daga kasashen duniya zuwa Najeriya yin kasuwanci ba.

Ya kara da cewa, masu saka hannayen jari sun san cewa a lokutan da kalubale yayi yawa ne ake samun damammaki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Adesina ya yi jawabi kan alfanun ziyarar aikin kwana hudu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai Dubai, Hadaddiya Daular Larabawa inda ya halarci taron Expo 2020.

A yayin karin jawabi, Adesina ya ce shugaban kasan ya yi daidai inda yace Najeriya ce wurin da ya fi dacewa da masu zuba hannayen jari a Afrika.

A yayin da aka tambaye shi ko masu zuba hannayen jari za su iya zuwa su narka kudadensu a Najeriya duk da kalubalen tsaro, Adesina yace:

Kara karanta wannan

Bidiyon sanatan Najeriya yayin da yake aikin sarrafa cunkoson ababen hawa a Abuja

"Idan har ka na tunani kamar mai zuba hannun jari, za ka gane cewa gara ka zuba kudin ka a inda babu zaman lafiya. Saboda idan ka zuba kudin ka a wurin da ke da matsala, za ka samu alheri mai yawa saboda matsalar nan bayan komai ya lafa."

Buhari ya sha alawashin ladabtar da masu daukar aikin gwamnati ba bisa ka'ida ba

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin daukan mataki tsatsaura kan duk wasu ma'aikatan gwamnati da ke da hannu wurin take dokokin gwamnatin tarayya ta hanyar daukar aiki ba bisa ka'ida ba tare da rufe ma'aikatan bogi.

Shugaban kasa Buhari wanda ya yi jawabin ne a taron bajekoli karo na uku na yaki da rashawa a fannin ayyukan gwamnati, wanda hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta (ICPC) tare da hadin guiwar ofishin sakataren gwamnatin tarayya suka shirya.

Buhari ya koka kan yadda ake daukar aikin gwamnati ba bisa ka'ida ba tare da rufe asirin ma'aikatan bogi wanda ya janyo hauhuwar kudin da gwamnati ke kashewa wanda ke illa ga tattalin arzikin kasar nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya taya ministansa murnan cika shekaru 70

Asali: Legit.ng

Online view pixel