Zina ba babban laifi bane, kiyayya da girman kai sun fishi muni: Cewar Paparoma

Zina ba babban laifi bane, kiyayya da girman kai sun fishi muni: Cewar Paparoma

  • Paparoma Francis ya yi tsokaci kan Babban limamin Katolikan da yayi murabus kan zargin yin Zina
  • Shugaban cocin Katolikan yace ya amince da murabus da Limamin yayi duk da Zina ba shine laifi mafi muni ba
  • A al'adar Katolika, bai hallata manyan malamai su kwanta da mace ba

Grika - Shugaban Cocin Katolika na duniya, Paparoma Francis, ya bayyana cewa zinar mai aure ba shi ne laifi mafi muni ba.

Independent UK ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai ranar Litinin cikin jirgi yayinda ya nufi Italiya daga Girka.

Paparoma yace laifukan da sassan jiki ke aikatawa basu bane laifuka mafi muni, innama kiyayya da girman kai sun fi shi muni.

Jawabinsa ya biyo bayan murabus din Archbishop na Faransa, Michel Aupetit, wanda aka yiwa zargin Zina da wata mata.

Kara karanta wannan

Dala daya (N409.89) na biya kudin sadaki, Matashin da ya auri yar shekara 70

Paparoma yace ya amince da murabus din Michel Aupetit ne saboda ya saba umurnin Injila, riwayar DailyMail.

Yace:

"Ya yi kuskure, kuma ya saba umurni na shida (a littafi), amma ba gaba daya ba."

Paparoma Francis
Zina ba babban laifi bane, kiyayya da girma kai sun fishi muni: Cewar Paparoma

Menene al'adar Kiristocin Katolika?

A al'adar Katolika, bai hallata manyan malamansu su kwanta da mace ba.

Archbishop Michel Aupetit, wanda ya saba wannan al'ada ya musanta zargin kuma yace:

"Ban tafiyar da lamari na da yarinyar da muke haduwa sosai yadda ya kamata ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel